A sakon da ya aike game da ranar samar da zaman lafiya, Mr. Ban ya lura da cewa, tashin hankali batu ne da ba shi da fa'ida, illa haifar da rashin adalci, nuna bambanci, da gallazawa, don haka kamata ya yi a neman mutuntawa da kare 'yancin bil-adama.
A ranar 2 ga watan Oktoban ko wace shekara ce ake yin bikin ranar yaki da tashin hankali ta kasa da kasa, don tuna ranar da aka haifi Mahatma Gandhi, jagoran kwatar 'yancin kasar India, wanda shugabannin kasashe a duniya suka yi amfani da dabaru da akidunsa na adawa da tashin hankali.
Don haka, Mr. Ban Ki-moon yake kira ga jama'a ko ina suke a wannan duniya da su yi koyi da karfin hali irin na Mahatma Gandhi, kana su yi watsi da nuna bambance-bambance da rashin nuna kauna, kana su tsaya ga nuna gaskiya da sanin ya kamata tare da rungumar hanyar sasantawa cikin lumana maimakon tashin hankali. (Ibrahim)