Kwamitin ya jaddada cewa, tilas ne a yanke hukunci ga wadanda suka shirya da aikata da kuma goyon bayan wannan mummunan laifi. Har ila yau sanarwar ta kalubalanci kasashen duniya da su bi dokoki da ka'idojin kwamitin sulhu, su kuma yi hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Afghanistan don warware wannan kalubale.
Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya nanata cewa, duk wani nau'in aikin ta'addanci zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya, kana laifi ne da ba za a amince da shi ba. Kuma bai kamata a alakanta ta'addanci da kowane addini, ko kasa, ko al'adu, ko kuma kabila ba.
A safiyar ranar 13 ga wata ne dai aka kai hari ga ginin karamin ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Afghanistan dake arewacin kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 5, kana mutane 23 sun ji raunuka. Tuni dai kungiyar Taliban dake kasar ta Afghanistan ta dauki alhakin gudanar da wannan hari. (Zainab)