in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin bincike kan makamai masu guba na MDD ya tashi daga Syria
2013-10-01 16:36:14 cri
A ranar Litinin 30 ga watan Satumba, bayan kammala aikinsa, rukunin masu binciken batun makamai masu guba na Syria na MDD ya tashi daga birnin Damascus, babban birnin kasar ta Syria.

A wannan rana, kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, yanzu babban aikin rukunin shi ne kammala wani rahotonp dake dauke da dukkanin bayanai kuma ana kiyasin cewa, za a kammala rahoton a karshen watan nan na Oktoba.

Bugu da kari, Nesirky ya yi bayanin cewa, rukunin ya samu taimako sosai daga Syria a wannan karo, shi ya sa ya samu bayanai da dama daga kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China