Kwamitin sulhu na MDD ya gabatar da wata sanarwa a ran 14 ga wata, inda ya la'anci hare-hare sau biyu da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan a 'yan kwanakin baya.
Sanarwar ta ce, ranar 11 ga wata, sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD da AU suka tura wa yankin Darfur wato UNAMID sun gamu da farmaki daga wasu dakaru da ba a san asalinsu ba a garin Al-Fashir na jihar Arewacin Darfur, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar wani mai sa ido kan aikin soja, 'dan asalin Zambiya. Ban da wannan kuma, a ranar 13 ga wata, ayarin motoci na UNAMID ya gamu da farmaki a garin Geneina na jihar West Darfur, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku, tare da raunanar guda daya, kuma dukkansu hudu 'yan asalin Senegal ne. Kwamitin sulhun MDD ya soki lamarin da kakkausar murya.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhu ya nuna jejeto ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu yayin hare-haren, da UNAMID, da kuma gwamnatocin Zambiya da Senegal. Shi kuma ya sake jaddada goyon bayansa kan ayyukan da UNAMID take gudanarwa, tare da yin kira ga bangarori daban daban na Darfur da su hada kansu da UNAMID yadda ya kamata. (Danladi)