13afirka
|
Ranar 25 ga watan Maris, shugaban dakarun kawancen Seleka na masu adawa da gwamnatin Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia, ya sanar da dakatar da tsarin mulkin kasar, da wargaza majalisar dokokin kasar, ya kuma yi alkawarin gudanar da zabe a shekaru 3 masu zuwa. Kafin kaiwa ga gudanar da zaben, ya ce shi zai tafiyar da harkokin kasar ta hanyar ba da umurni. A ranar 21 ga watan Maris, dakarun Seleka sun zargi shugaban kasar Francois Bozize dagaza aiwatar da yarjejeniyar Libreville, matakin da ya sanya su daukar matakin soja. A ranar 24 ga watan Maris, dakarun Seleka sun mamaye birnin Bangui, wanda ya tilasa shugaban kasar Francois Bozizé tserewa zuwa kasar Kamaru, kafin daga bisani Michel Djotodia ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar.