in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya soki juyin mulkin da 'yan tawayen Afirka ta Tsakiya suka gabatar
2013-03-26 15:36:43 cri
Ran 25 ga wata da dare, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa ga kafofin watsa labarai, inda ya yi suka da kakkausar murya ga aikace-aikacen tashin hankali da juyin mulkin kasa da aka gabatar a jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya cikin kwanankin nan.

A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya yi tattaunawa game da yanayin da ake ciki a jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya, daga bisani kuma ya ba da sanarwa ga kafofin watsa labarai, inda ya nuna rashin jin dadi matuka ga aikace-aikacen tashin hankali da suka faru a kasar Afirka ta Tsakiya, musamman ma wadanda suka haddasa jikkatar ko kuma rasuwar sojojin Afirka ta Kudu da aka aike zuwa kasar bisa kiran gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya.

Sanarwa ta kuma bayyana cewa, matakan da shugabannin kawancen dakarun Seleka, masu adawa da gwamnatin jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya suka dauka, sun saba wa yarjejeniyar Libreville, kana suna barazana ga kawo yanayin zaman karko a kasar.

Don haka, kwamitin sulhu zai ci gaba da sa ido kan yanayin kasar, zai kuma dauki karin matakai idan akwai bukatun yin hakan.

Haka zalika a cikin wannan rana, kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan Afirka ta Tsakiya a cikin kungiyar, za ta kuma dorawa shugabannin 'yan tawayen kasar takunkumi da za su hada da hana su tafiya zuwa kasashen ketare, da kuma toshe kafofinsu na kudade da kadararsu.

A wannan rana da dare, shugaban kungiyar Seleka mai adawa da gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia ya kira wani taron manema labarai, inda ya sanar da dakatar da tsarin mulkin kasa, rusa majalisar dokokin kasar, kana ya sanar da cewa, kafin a gudanar da babban zaben kasa, zai gudanar da ayyukan mulkin kasa ta hanyar bayar da dokoki da kansa. Bugu da kari, ya kuma sanar da dokar hana fitar dare tun karfe bakwai da yamma zuwa karfe shida da rabi da safe a duk fadin jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China