Mista Ban na nuna damuwa sosai kan yawan hare-hare da ayyukan keta hakkin dan Adam kan musulmi da kristoci, har ma haduran da suka faru na baya baya a kan hanyar Bossangoa zuwa Bossembele, in ji wannan sanarwa tare da kara bayyana cewa babban sakatare-janar MDD ya yi babbar suka kan wadannan hare hare.
Haka kuma mista Ban ya bukaci tsoffin 'yan tawayen Seleka, gungun kungiyoyi masu makamai da sauran bangarori daban daban da su kaucewa kan hare-hare kan fararen hula da kuma girmama 'yancin dan Adam, tare da yin kira kuma ga hukumomin kasar Afirka ta Tsakiya da su gurfanar dukkan masu hannu kan tashe-tashen hankali da cin zafarin dan Adam da kuma kare jama'ar kasa daga wadannan hare-hare.
Tun lokacin da tsohon shugaban kasar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize ya yi ta kokarin karbe ikonsa a cikin watan Augusta, kimanin mutane dari ne aka kashe a cikin watan Satumba a cikin fadace fadace tsakanin magoya bayan mista Bozize da kuma dakarun dake marawa shugaban wucin gadi Michel Djotodia.
Wannan kasa dake tsakiyar Afrika ta fada cikin wani mawuyacin hali tun lokacin da 'yan tawayen Seleka suka karbe Bangui, babban birnin kasar tare da kawar da shugaba Bozize daga mulki a cikin watan Maris. (Maman Ada)