in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen Seleka sun kutsa kai babban birnin janhuriyar Afirka ta Tsakiya
2013-03-24 16:12:29 cri
Da yammacin ranar Asabar 23 ga watan nan ne mayakan kungiyar 'yan tawayen Seleka suka kutsa kai yankunan babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya wato Bangui, a yunkurinsu na kame fadar mulkin kasar.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya bayyana cewa, dakarun sun yi arangama da sojojin gwamnatin kasar, wadanda ke samun goyon bayan rundunar sojin kasar Afirka ta Kudu. Tuni dai bangaren sojojin gwamnatin da ake wa lakabi da FACA suka ja daga a fadar gwamnati domin ba ta kariya. Wasu rahotanni ma sun bayyana cewa, an katse wutar lantarki a dukkanin yankin da fadar shugaban kasar take.

An kuma ce ma'aikatan MDD dake birnin na Bangui na can wani sansani dake samun kariya daga hukumomin kasa da kasa, a shirin da ake yi na kwashe su ta filin jirgin saman yankin Bangui-Mpoko.

A wani labarin mai alaka da wannan, kasar Faransa ta bayyana shirinta na tura sojoji zuwa kasar Afirka ta Tsakiya, domin tabbatar da kwashe 'yan kasarta dake birnin na Bangui.

Matakin sojin da dakarun Seleka ke dauka a wannan lokaci dai ya biyo bayan zargin da suka yi na cewa, gwamnatin Afirka ta Tsakiyar ta ki martaba yarjeniyoyin da aka kulla a watan Janairun da ya gabata, ciki har da batun sakin firsunonin siyasa, da shigar da dakarunta cikin rundunar sojin kasar, da kuma ficewar sojojin kasashen Afirka ta Kudu da na Uganda wadanda ke bai wa gwamnatin kariya. Baya ga zargin kin martaba makamanciyar wannan yarjejeniya da aka gudanar a birnin Libreville na kasar Gabon tun cikin shekara ta 2007.

A 'yan kwanankin baya ne shugaban kasar ta Afirka ta Tsakiya Francois Bozize ya kai wata ziyara Afirka ta Kudu, inda ya bukaci kasar da ta taimakawa kasar tasa da karin dakarun soji, domin kare mamayar 'yan tada kayar bayan.

Shugaba Bozize da ya dare karagar mulkin kasar a shekarar 2003 na fuskantar kalubale daga dakarun hadakar kungiyar ta Seleka, wadda ke kunshe da bangarorin 'yan adawa 5, wadanda kuma ke ci gaba da barazana ga dorewar gwamnatin kasar ta hanyar kai hare-hare daga kudancin kasar tun daga ranar 10 ga watan Disambar bara.

A baya dai dakarun Seleka sun gaza kaiwa yankin Damara hari ne, sakamakon tungar da dakarun hadin gwiwar kasashen tsakiyar nahiyar Afirka na CEEAC suka yi tsakanin birnin Bangui da kuma inda 'yan tawayen suka yi sansani. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China