in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afirka ta Tsakiya: Michel Djotodia ya yi alkawarin mika mulki nan da shekaru uku masu zuwa
2013-03-31 17:08:10 cri
Mutumin da ya nada kansa matsayin shugabancin kasar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia, ya yi shelar cewa, zai mika mulkin kasar ga zababbiyar gwamnati nan da shekaru uku masu zuwa. Djotodia ya yi wannan tsokaci ne a jiya Asabar, yayin wani taro da aka gudanar a babban birnin kasar Bangui.

Firaministan hadaddiyar gwamnatin kasar da Djotodia ya nada, da wasu tsoffin ministocin hadaddiyar gwamnatin kasar, da dakarun Seleka, da kuma wasu mutane sama da dubu daya ne suka halarci wannan taro. Djotodia ya yi jawabinsa da harshen Sango, inda ya yi alkawarin mayar da tsarin zaman lafiya a birnin Bangui, da ma duk fadin kasar baki daya. Haka nan ya yi kira ga jama'ar kasar da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba, tare da yin kira ga 'yan gudun hijira, da su dawo kasar ta Afirka ta Tsakiya.

Dadin dadawa, Djotodia ya yi alkawarin cewa, ba zai mai da martani ga wadanda suka yi adawa da shi ba. Ban da haka, sabon shugaban cewa, zai kawar da sojojin LRA daga kasar cikin watanni uku masu zuwa.

Tun dai shekaru 90 na karnin da ya gabata kawo yanzu, sojojin LRA ke ta da zaune-tsaye a arewacin Uganda, yayin da kuma wasunsu ke tada hankula a yankunan dake kan iyakokin kasashen Sudan ta Kudu, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kango, da kuma Afirka ta Tsakiya.

A nasa bangare, wani mai magana da yawun majalisar zartaswar kasar Amurka, ya ba da sanarwar a ranar Asabar 30 ga wata, dake Allah wadai da kwace mulkin kasar Afirka ta Tsakiya da wasu dakaru masu adawa da gwamnatin suka yi. Jami'in ya yi kira ga bangarori daban daban da lamarin ya shafa, da su ci gaba da kokari, da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Sanarwar ta ce, a sa'i daya Amurka na zargin shugaban kungiyar Seleka, Michel Djotodia, don gane da nada kansa da yayi a matsayin shugaban kasar Afirka ta Tsakiya, tare da dakatar da amfani da kundin tsarin mulkin kasar, da wargaza majalisar ministoci da yayi. Sanarwar ta yi kira da jagororin kasar, da su kafa wani tsari na zahiri, bisa dokoki masu nagarta cikin sauri, kafin gudanar da babban zaben kasar.

Baya ga hakan, sanarwar ta yi kira ga kasashe membobin kungiyar gamayyar tattalin arziki ta kasashen tsakiyar Afirka,da su ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a kasar ta Afirka ta tsakiya.

Tun dai ranar 10 ga watan Disambar bara ne kungiyar Seleka ta fara daukar matakan soja a kasar, tare da bukatar shugaba Bozize da ya sauka daga mukaminsa. Sa'annan a ranar 11 ga watan Janairun bana, gwamnatin kasar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar ta Seleka a birnin Libreville, hedkwatar kasar Gabon, inda aka amince da kafa hadaddiyar gwamnatin kasar ta rikon kwarya. Amma a ranar 21 ga watan Maris din nan, kungiyar Selekan tayi watsi da waccan yarjejeniya, tare da sake daukar makamai domin yakar sojin gwamnati, bisa zargin gwamnatin na kin martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.

A ranar 24 ga wata, Seleka ta mamaye birnin Bangui, bayan da shugaba Bozize ya arce zuwa kasar Kamaru. Daga bisani kuma a ranar 25 ga wata, shugaba Seleka, Djotodia ya nada kansa a matsayin shugaban kasar Afirka ta Tsakiya. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China