A ranar 6 ga watan nan ne ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, da hukumar abinci ta duniya, da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, suka bayyana aniyar daukar wannan mataki yayin wani taron manema labarai a birnin Geneva. Hukumonin sun kuma shan alwashin ba da taimako ga jamhuriyar Afirka ta Tsakiyan a fannonin agajin jin kai, sakamakon tashe-tashen hankula da kasar ke fuskanta a halin yanzu. (Maryam)