in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Michel Djotodia ya zama shugaban kasar Afirka ta Tsakiya na wucin gadi
2013-04-14 17:12:10 cri
A ranar Asabar 13 ga wata, kwamitin rikon kwarya na kasar Afirka ta Tsakiya, ya nada Michel Djotodia, shugaban kungiyar Seleka, wadda ta yi adawa da gwamnatin Francois Bozizé a matsayin shugaban kasar na wucin gadi, inda aka bayyana cewa zai kasance bisa ragamar mulkin kasar tsawon watanni 18.

A wannan rana ne kuma kwamitin ya kira taro karo na farko, inda aka kaddamar da Michel Djotodia a matsayin shugaban kasar na wucin gadi, inda nan take mambobin kwamitin suka amince da haka, tare da yin tafi domin nuna farin cikin su da wannan mataki. Daga bisani, Djotodia ya yi gajeren jawabi da harshen Faransanci da kuma yaren Sango, inda ya yi shelar cewa, abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, tabbatar da zaman lafiya da farfado da tattalin arziki a kasar ta Afirka ta Tsakiya.

An kafa kwamitin rikon kwarya na kasar Afirka ta Tsakiya ne dai a ranar 11 ga watan nan, wanda ya kunshi membobi 105, ciki hadda 'yan kungiyar Seleka, da sauran manyan jam'iyyun kasar da dai sauransu. Kwamitin ya dauki nauyin gudanar da ayyukan majalisar wakilan kasar ta wucin gadi. Har ila yau, a ranar 3 ga wata ne, yayin taron koli na musamman, na tinkarar matsalar kasar Afirka ta Tsakiya, da kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta yi, an ba da shawara kan kafa wannan kwamiti a kasar Afirka ta Tsakiya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China