Shugaban kasar Kongo Brazzaville, Denis Sassou-N'guesso, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, firaministan kasar Afirka ta Tsakiya, Nicolas Tiangaye, wakilan kungiyar AU da na MDD da dai sauransu sun halarci wannan taro.
Mahalarta taron suna ganin cewa, rikicin Afirka ta Tsakiya barazana ne ga zaman lafiya da tsaron shiyya-shiyya da ma na duniya baki daya, a sabili da haka, kamata ya yi a dauki matakai, a kokarin neman samun wani shirin share fagen warware wannan rikici na dogon lokaci.
A gun taron, an zartas da wani kuduri da aka kira "Kira ga Brazzaville", inda aka bukaci jam'iyyu daban daban na kasar da su tabbatar da yarjejeniyar siyasa ta Libreville da sanarwar N'Djamena nan take, tare da kalubalantar su dangane da farfado da yin shawarwari cikin hakuri, a kokarin samar da wani kyakkyawan yanayi, da zummar sa kaimi ga samun daidaito a duk fadin kasar.
Bisa kudurin na "Kira ga Brazzaville", tawagar za ta yi hadin gwiwa da bangarori daban daban na kasar Afirka ta Tsakiya, a kokarin samar da kariya ga fararen hula, gami da tabbatar da ba da agajin jin kai a kan lokaci, da kuma taimakawa kasar wajen sake kafa ikon tsaron kasa.(Fatima)