A ranar 18 ga wata, Michel Djotodia, tsohon shugaban kawancen dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na "Seleka" ya yi rantuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasar, kuma a matsayin shugaba na shida tun bayan da ta samu 'yancin kanta yau da shekaru 53 da suka gabata.
A cikin shekaru fiye da l0 da suka wuce, kasar Afirka ta Tsakiya ta rika fuskantar tashe-tashen hankalin siyasa, da suka janyo juyin mulki sau da yawa a wannan kasa. A watan Disamba na bara, kawancen dakaru na Seleka ya shelanta tawaye da gwamnatin kasa tare da tada rikici a arewacin kasar, lamarin da ya kai ga karbe iko bayan da kawancen Seleka ya shiga Bangui, hedkwatar kasar a watan Maris na bana. A ranar 13 ga watan Afrilu kuma, kwamitin wucin gadi na kasar ya zabi mista Djotodia a matsayin shugaban wucin gadin kasar, wanda wa'adin aikinsa ya kai watanni 18.
Bayan da Mista Djotodia ya hau kan karagar mulkin kasar, matsala mafi girma dake gabansa ita ce ta yadda za a samu kwanciyar hankali a wannan kasar da ke fama da kangin talauci. Shugaban kasar na Afrika ta Tsakiya ya yi alkawari a bikin rantsuwar kama aikinsa, cewar dole ne zai yi kokari don tabbatar da zaman lafiya, da samun dinkulewar kasar wuri daya, ta yadda jama'ar kasar Afirka ta Tsakiya za su ji dadin zaman rayuwarsu.
Tun bayan barkewar tawayen kungiyar Saleka, kawo yanzu mutanen kasar dubu 206 sun bar gidajensu, daga cikinsu mutane dubu 62 sun yi gudun hijira a Jamhuriyar Demokuradiyar Kongo da kasar Chadi da dai sauran kasashen da ke makwabtaka da Afirka ta Tsakiya.(Kande Gao)