Wata sanarwar da kakakin babban sakataren ya fitar, ta rawaito Mr. Ban na cewa, bata kashi da sassan al'ummar kasar Musulmi da Kirista, da ma ragowar dakaru masu dauke da makamai ke yi, na nuni ga irin hadarin da kasar ke fuskanta. Don haka Mr. Ban ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su kai zuciya nesa, su kuma kauracewa goyon bayan masu rura wutar rikici. Ya ce, hakika dukkanin masu hannu cikin wannan aika-aika za su fuskanci tuhuma gaban kuliya.
Bugu da kari sanarwar ta jaddada matukar bukatar daukar matakan ba da kariya ga fararen hular kasar, da samar da agaji ga wadanda suka tsinci kansu ckin mawuyacin hali, tare kuma da tabbatar da komawar kasar kan turbar tsarin mulki da doka ta tanada, kamar yadda hakan ke kunshe cikin kudurin da ya kafa gwamnatin rikon kwaryar kasar. (Saminu)