in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara dubu 600 ne rikicin Afirka ta tsakiya ya shafa, in ji UNICEF
2013-03-27 10:49:40 cri

Asusun harkokin yara na MDD, UNICEF ya bayyana ranar Talata cewa, yara kusan dubu 600 ne rikicin kasar Afirka ta tsakiya ya shafa.

Yayin wata ganawa da manema labarai, mai magana da yawun asusun Marixie Mercado ta bayyana cewa, a cikin watanni uku da suka gabata, al'ummomi na cikin yankuna dake hannun 'yan tawayen ba su samun muhimman ababai kamar kiwon lafiya da ilmi.

A kalla yara kusan dubu 166 ne aka tarewa damar samun ilmi domin makarantu suna rufe, inda dakarun ke zaune cikinsu kuma babu malamai, kana yara kusan dubu 13.5 ne ake ganin cewa, za su fuskanci matsalar karancin abinci a wannan shekara, in ji asusun.

Mercado ta kara da cewa, daukar yara kanana a soja na daga cikin sauran manyan barazana.

A halin yanzu dai ayyukan jin kan bil adama na fuskantar cikas saboda rashin kudade, in ji jami'ar.

Cibiyoyin taimakon bil adama sun kaddamar da asusun neman taimakon dalar Amurka miliyan 129 don ayyukan gaggawa a shekarar 2013 a kasar ta Afirka ta Tsakiya, to amma zuwa yanzu dai kashi daya daga cikin dari na wannan adadi ne aka samu, in ji UNICEF.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China