Wani mai shiga tsakani kan batun kungiyar Seleka ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa, 'yan tawayen Seleka sun riga sun kame fadar shugaban kasar dake birnin Bangui, hedkwatar kasar Afirka ta Tsakiyar.
Ya kara da cewa, "Mulkin shugaba Bozize ya kare a wannan gaba, musamman a wannan lokaci da 'yan tawayen Selekan ke ci gaba da kai hare-hare kan sansanin sojin kasar, da sauran muhimman wurare dake birnin Bangui." A cewarsa ana bukatar mazauna birnin su kasance cikin gidajensu domin samun zarafin maido da daidaito da tsari a birnin.
Wani mazaunin birnin ya bayyana wa 'yan jarida ta wayar tarho cewa, a safiyar Lahadin nan 'yan tawayen Seleka suka rika kai hare-hare, suka kuma kutsa kai cikin birnin Bangui. Kawo yanzu dai, rahotanni na cewa, wasu motocin soja masu tambarin rundunar mayakan Seleka na sintiri a manyan titunan birnin. (Fatima)