in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwarta dangane da kara matsowar 'yan tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
2013-03-23 16:27:59 cri
A ranar Jumma'a ce kwamitin sulhu na MDD da magatakarda Ban Ki-Moon suka nuna damuwa matuka dangane da rahotannin dake nuna cewa 'yan tawaye na kara matsowa Bangui babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) bisa la'akari da abin da hakan zai haifar ga bil adama a kasar dake fama da rikici.

Kwamitin sulhun ya yi tir da dukkan yunkurin gunguntar da dorewa a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tare kuma da yin kira ga dukkan bangarori su ajiye makamai, inji wata sanarwa da aka bayar bayan da mambobin kwamitin suka saurari rahoto daga mataimakin magatakardan MDD kan harkokin siyasa Taye-Brook Zerrihoun, dangane da hali da ake ciki a kasar.

A ranar jumma'a ce gammayar kungiyar 'yan tawayen Seleka ta yi kirarin kama garuruwan Bossangoa da Damara dake da nisan kilomita 75 da kofar shiga birnin Bangui.

Suna barazanar kifar da shugaba Francois Bozize da gwamnatin da aka kafa a watan da ya wuce, saboda a fadar 'yan tawayen, gwamnatin ba ta aiwatar da yarjejeniya da aka rattaba hannu kanta ba a ran 11 ga watan Janairu a garin Libreville, babban birnin kasar Gabon.

A cikin wata sanarwa, kwamitin sulhu na MDD mai mambobi 15 ya yi kira ga dukkan bangarori da su kauracema cin zarafin farar hula, su kuma bari a yi aikin tallafawa bil adama cikin sauki kana su kiyaye 'yancin bil adama da dokokin 'yancin bil adama na kasa da kasa.

A sanarwa da ya bayar ta hannun mai Magana da yawunsa, magatakardan na MDD Ban Ki-Moon ya yi kira ga 'yan tawayen Seleka da su dakatar da dukkan wata harka ta fada, kana dukkan bangarori su kiyaye yarjejeniya da aka kulla a Libreville.

Ban ya kuma lura da cewa, MDD za ta ci gaba da bada goyon baya ga kokarin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen da ke tsakiyar nahiyar Afirka(ECCAS) da dai sauransu don tabbatar da ganin an warware rikicin cikin lumana.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China