Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci a daina aikace-aikacen tayar da hakulan jama'a a kasar Afirka ta Tsakiya
Ran 14 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa inda ya nuna damuwarsa dangane da tabarbarewar yanayin tsaro da harkokin jin kai, abin da ya sa ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa a kasar Afirka ta Tsakiya da su daina aikace-aikacen tayar da hakulan jama'a a kasar.
Cikin sanarwar, kwamitin sulhu na MDD ya jaddada cewa, gwamantin kasar na da hakkin kiyaye tsaron jama'ar kasar, ya kamata a dakatar da rikice-rikice a kasar, baiwa kungiyoyin kare hakkin dan Adam damar shiga yankunan kasar don ba da agaji da kuma nuna girmamawa ga dokar tausaya wa bil-Adam na duniya da kuma dokar kare hakkin dan Adam. (Maryam)