in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
• An rufe taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya" a nan Beijing 2017-05-16
Da yammacin jiya Litinin 15 ga wata ne aka rufe taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya", wanda aka yi kwanaki 2 ana yinsa a nan Beijing. A lokacin da yake ganawa da manema labarum gida da na waje, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, an cimma matsaya daya, a bangarori daban daban a yayin taron, an kuma samu hanyar yin hadin gwiwar kasa da kasa, da tabbatar da shirin aiwatarwa na bunkasar "ziri daya hanya daya". Bugu da kari, a yayin taron, an samu wata kyakkyawar alama, wato bangarori daban daban na kasashen duniya na kokarin yin hadin gwiwar ciyar da bil Adama gaba, ta hanyar bunkasa "ziri daya hanya daya". Sannan Shugaba Xi Jinping ya shelanta cewa, kasar Sin za ta shirya taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya" karo na biyu a shekarar 2019...
• An yi taron shugabannin dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya" a Beijing 2017-05-15
Yau Litinin ne aka shiga kwana na biyu na babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa game da "ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing, inda shugabannin kasashe mahalarta dandalin suka halarci wani muhimmin taro. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron, inda ya jadddada cewa, shawarar "ziri daya hanya daya" ta samo asali ne daga kasar Sin, amma shawara ce ga dukkanin kasashen duniya, kuma kofa a bude take ga duk mai son shiga wannan shawara.
• Xi Jinping: Shawarar "Ziri daya hanya daya" wani zabi ne mai dacewa wajen samar da makoma mai haske 2017-05-15

Jiya Lahadi ranar 14 ga wata, an kaddamar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing. A daren ranan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shirya liyafa, don maraba da zuwan baki mahalarta taron daga kasashe daban daban. A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya hanya daya" ta kunshi burinmu na kara cudanya a tsakanin al'adu daban daban, da na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, da na neman ci gaba gaba daya, gami da na neman jin dadin zaman rayuwa. Muddin mu yi kokari tare, tabbas ne sha'aninmu zai amfana wa zuriyoyinmu kamar yadda hanyar siliki ta zamanin da...

• An bude babban taron dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya" a Beijing 2017-05-14
Yau Lahadi, a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, aka kaddamar da babban taron dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya", inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "raya 'ziri daya hanya daya' kafada da kafada"...
• Wakilin Habasha dake MDD: Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta biya bukatun ci gaban duniya  2017-05-12

A Laraba 10 ga wata ne, zaunannen wakilin kasar Habasha dake MDD Tekeda Alemu ya gaya wa manema labarai a birnin New York na kasar Amurka cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta biya bukatun ci gaban kasashen duniya, duk da cewa kasar Sin ce ta bullo da shawarar, amma tana shafar muradun daukacin kasashen duniya, saboda shawarar ta jaddada cewa, yana muhimmanci a samu ci gaba tare bisa tushen adalci da moriyar juna...

• Shugaban kasar Kenya: Shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta taimakawa hadin gwiwar Afirka da Sin 2017-05-11
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai halarci taron dandalin koli da za a kira a nan birnin Beijing, daga ranar Lahadi zuwa Litinin mai zuwa, inda za a tattauna hadin gwiwar kasa da kasa karkashin laimar shawarar "ziri daya da hanya daya"...
• Magatakardan MDD: Shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta nuna dabarar kasar Sin wajen sa kaimi ga ci gaban duniya  2017-05-10

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai kawo wa kasar Sin ziyara daga ranar 13 zuwa ranar 15 ga wata, sa'an nan zai halarci taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya" wanda za a yi a birnin Beijing. Wannan ne karo na farko da Mr. Guterres zai kawo wa Sin ziyara tun bayan da ya hau kujerar magatakardan MDD...

• Manyan kamfanonin Sin sun ba shirin "Ziri daya da hanya daya" muhimmanci 2017-05-09

Tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", manyan kamfanonin kasar wadanda ke karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar suka ba shirin muhimmanci matuka, inda har suka ba da gudummowarsu ga aikin aiwatar da shirin...

• Babban jami'in WIPO: Shirin "Ziri daya da hanya daya" salon hadin gwiwa ne mai inganci 2017-05-08

Kwanakin baya babban jami'in hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya WIPO Francis Gurry ya zanta da wakilin gidan rediyon CRI kafin ya tashi zuwa nan birnin Beijing domin halartar dandalin hadin gwiwa game da shirin "Ziri daya da hanya daya", inda ya bayyana cewa, shirin wani nau'in hadin gwiwa ne mai inganci wanda zai kawo babbar moriya ga kasashen da abin ya shafa...

• Masanin Kenya: shirin "Ziri daya da hanya daya" zai taka rawa ga ci gaban kasashen Afirka  2017-05-05

Za a gudanar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shirin "Ziri daya da hanya daya" a tsakiyar watan Mayun da muke ciki a nan birnin Beijing, kafin wannan, daraktan cibiyar nazarin manufofin raya kasashen Afirka ta kasar Kenya Robert Kagiri ya zanta da wakilin gidan rediyonmu a birnin Nairobi, inda ya bayyana cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" ya samar da wata sabuwar dama ga hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, haka kuma dandalin da za a kaddamar zai kasance wani gaggarumin bikin da zai jawo hankalin al'ummomin kasashe a fadin duniya...

• Nan gaba kadan layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya zai dawo hayyacinsa 2017-05-03
Idan muka yi waiwaye, za mu gano cewa, an shimfida layin dogon da ya hada kasashen Tanzaniya da Zambiya a lokacin da ake kokarin 'yantar da al'umma a kudancin nahiyar Afirka. Amma bayan shafe dogon lokaci, a wani irin yanayin da layin dogon ke ciki a halin yanzu?
• Hanyar dogo ta SGR da ta tashi daga Mombasa-Nairobi za ta soma aiki a watan Yunin bana 2017-05-02
Kasar Kenya muhimmiyar kasa ce a fannin hadin kai bisa manyan tsare-tsare dangane da shirin nan na "Ziri daya hanya daya" a tsakanin Sin da kasashen Afirka, Haka kuma tana daya daga cikin kasashen dake sahun gaba a fannin gwajin hadin kan samar da kayayyaki tsakanin Sin da kasashen Afirka. Hanyar dogo ta SGR hanya ce da ta hade Mombasa wato tashar jiragen ruwa mafi girma a gabashin Afirka, da Nairobi babban birnin kasar Kenya. Bayan kafuwar hanyar dogon za a samu sauye-sauye a garuruwan dake dab da ita...
• Ana fatan layin dogo na Tanzania da Zambiya zai sake taka rawa a sabon yanayin da ake ciki 2017-04-27
Layin dogo da ya hade kasashen Tanzania da Zambiya, layin dogo ne da kasar Sin ta tallafawa kasashen Afirka biyu wajen shimfida shi. Ya yi suna sosai a kasar Sin, sabo da yana alamtar zumuncin dake kasancewa tsakanin kasar Sin da kasashen Tanzania da Zambiya. A kwanan baya, wakilinmu dake aiki a Afirka, ya zanta da tsohon ministan harkokin wajen kasar Zambiya Vernon Mwaanga, mai shekaru 73 da haihuwa, wanda ya san tarihin shimfida wannan layin dogo sosai...
• Aikin gyara layin dogo dake hade kasashen Tanzania da Zambiya zai kawo karin damar bunkasa yankin tattalin arzikin Zambiya 2017-04-25
Yanzu haka ana tattaunawa kan yadda za a gyara, da kuma kyautata yanayin layin dogo dake hade kasashen Tanzania da Zambiya a tsakanin kasashen Sin da Zambiya da Tanzania. A wani yankin dake kusa da tashar karshe ta wannan layin dogo a kasar Zambiya, akwai wata shiyyar Chambishi, ta yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci da kasashen Zambiya da kasar Sin suka kafa. Sakamakon fuskantar matsaloli iri daban daban, layin dogo na Tanzania da Zambiya bai taka rawa kamar yadda ya kamata ba kan yankin da ake fata. Amma idan an gyara da kuma kyautata yanayin wannan layin dogo, tabbas zai taka muhimmiyar rawa ga wannan yanki na bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci...
• Shirin "ziri daya da hanya daya" na taimakawa ci gaban tattalin arzikin Afirka  2017-04-24

A 'yan kwanakin baya, aka kaddamar da bikin fara aikin wani kamfanin samar da siminti da kamfanin kasar Sin zai gina a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda firayin ministan kasar Hailemariam Desalegn ya jinjinawa taimakon da kamfanin na kasar Sin ke baiwa kasarsa, wajen samar da siminti...

1  2  
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China