in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya" a nan Beijing
2017-05-16 10:16:47 cri

Da yammacin jiya Litinin 15 ga wata ne aka rufe taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya", wanda aka yi kwanaki 2 ana yinsa a nan Beijing. A lokacin da yake ganawa da manema labarum gida da na waje, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, an cimma matsaya daya, a bangarori daban daban a yayin taron, an kuma samu hanyar yin hadin gwiwar kasa da kasa, da tabbatar da shirin aiwatarwa na bunkasar "ziri daya hanya daya". Bugu da kari, a yayin taron, an samu wata kyakkyawar alama, wato bangarori daban daban na kasashen duniya na kokarin yin hadin gwiwar ciyar da bil Adama gaba, ta hanyar bunkasa "ziri daya hanya daya". Sannan Shugaba Xi Jinping ya shelanta cewa, kasar Sin za ta shirya taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya" karo na biyu a shekarar 2019.

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, muhimman bakin gida da na waje fiye da 1500 ne suka tattauna bisa jigon taron, wato "kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin bunkasa 'ziri daya hanya daya' tare, ta yadda za a iya samun ci gaba tare".

A lokacin da yake ganawa da manema labarun gida da na waje, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, an cimma matsaya daya a yayin wannan taron kolin, har ma an samu hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen aiwatar da shawarar "ziri daya hanya daya" a nan gaba. Shugaba Xi ya ce, "Wannan wani gagarumin taron koli ne da aka shirya bisa shawarar 'ziri daya hanya daya' tsakanin kasa da kasa. A yayin taron, an tattauna kan yadda za a yi hadin gwiwa, an kuma cimma matsaya daya, har ma an samu hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, an tsara shiri da tabbatar da matakin aiwatar da shawarar 'ziri daya hanya daya'. Wannan taron ya samar da wata kyakkyawar alama, wato bangarori daban daban na kasashen duniya, na kokarin yin hadin gwiwar ciyar da bil Adama gaba ta hanyar bunkasa 'ziri daya hanya daya'."

Bayan da shugaba Xi Jinping ya fitar da wannan shawara ta "ziri daya hanya daya" a shekarar 2013, bisa ka'idar tattaunawa, da bunkasa, da kuma rarrabawa tare", bangarori daban daban wadanda suke amsar wannan shawara sun yi kokarin yin hadin gwiwa a fannonin daidaita manufofi, da hanzarta aiwatar da ayyukan tattalin arziki da cinikayya, da hade kayayyakin more rayuwar jama'a, da kuma saukaka sharuddan cinikayya da zuba jari. Al'ummomin kasa da kasa ma na kara yin mu'amala a tsakaninsu. Ya zuwa yanzu aikin bunkasa "ziri daya hanya daya" ya shiga wani sabon lokaci.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, "Za mu daidaita muhimman manufofin tattalin arziki wadanda za su shafi cinikayya da zuba jari, da hada-hadar kudi. Za mu kuma hanzarta yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, da kuma kafa wani kyakkyawan yanayin bunkasa duk duniya gaba daya. Bugu da kari, za mu fitar da shirye-shiryen neman ci gaba, wadanda za su dace da juna, sannan za mu tsara shirin aiwatarwa tare, domin samar da manufofi masu dacewa ga muhimman ayyuka. A waje daya, za mu kiyaye da kuma bunkasa tattalin arziki, wanda zai shafi duk duniya gaba daya. Har ila yau, ma za su hanzarta gina yankunan yin cinikayya cikin 'yanci, domin sa kaimi ga ayyukan yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci kuma cikin sauki."

A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya hanya daya", bangarori daban daban, sun kulla wasu takardun yin hadin gwiwa a fannonin kara daidaita manufofi, da hade ababen more rayuwa, da gudanar da kasuwanci maras kaidi, da hade sassan hada hadar kudi, da kulla alaka tsakanin al'ummu.

Ya zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka amince da takardun hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya hanya daya" da kasar Sin sun kai 68.

Game da muhimman fannonin yin hadin gwiwa a nan gaba, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, "Mun yarda da ci gaba da sa aikin haduwar juna a muhimmin matsayi na yin hadin gwiwa. Kuma za mu yi kokarin shimfida hanyoyin sufuri na kasa da na teku. Sakamakon haka, za mu iya kafa wani tsarin sufuri dake kunshe da tasoshin ruwa, da na sama da kasa. Sannan muna goyon bayan kokarin bunkasa zirin raya tattalin arziki, inda za mu kara yin hadin gwiwa a fannonin samar da makamashi, da injuna tsakanin kasa da kasa. Bugu da kari, za mu ci gaba da nuna goyon baya ga hadin gwiwar da ake yi a fannonin ba da ilmi, da kimiyya da fasaha, da al'adu da kiwon lafiya, da yawon shakatawa da kafofin yada labaru da dai makamatansu."

Daga karshe dai, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da hanzarta bunkasa "ziri daya hanya daya", da tinkarar kalubalolin tattalin arziki cikin hadin gwiwa da ake fuskanta a duk duniya baki daya, suna dacewa da moriyar kasashen duniya. Kuma ya kamata kasashen duniya su yi imani ga makomar "ziri daya hanya daya". (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China