in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya: Shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta taimakawa hadin gwiwar Afirka da Sin
2017-05-11 16:28:29 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai halarci taron dandalin koli da za a kira a nan birnin Beijing, daga ranar Lahadi zuwa Litinin mai zuwa, inda za a tattauna hadin gwiwar kasa da kasa karkashin laimar shawarar "ziri daya da hanya daya".

Kafin tashinsa daga kasar Kenya, shugaba Kenyatta ya gana da manema labaru ranar Talata da ta gabata.

Yayin taron manema labarun da aka kira a birnin Nairobi, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" na kunshe da burin hada yankuna daban-daban da layin dogo da hanyar mota, matakin da zai taimakawa dunkulewar yankunan nahiyar Afirka, tare da tabbatar da moriyar bai daya tsakanin bangarorin Afirka da Sin.

A cewar shugaban, yana da kyakkyawar fata kan ziyararsa a kasar Sin a wannan karon, domin zai halarci taron nan na tattauna shawarar "ziri daya da hanya daya" a madadin kasarsa ta Kenya.

Har ila yau, zai tattauna tare da sauran shugabannin kasashen Afirka, don ingiza aikin dunkulewar yankunan Afirka waje guda. Ya ce, yana sa ran ganin an samu nasarori da yawa a wajen taron, bisa wani tushe na kokarin tabbatar da moriyar dukkan bangarori, ban da haka kuma, za a samu kyautatuwar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, har ma da sauran kasashen nahiyar Afirka.

Shugaban na kasar Kenya na ganin cewa, matakin hada wurare daban- daban da karin yin mu'amala tsakaninsu dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya", zai taimakawa yunkurin dunkulewar yankunan nahiyar Afirka. Haka zalika, wani abun da ya kara ba muhimmanci shi ne manufar "hada kayayyakin more rayuwa a kasashe daban-daban" wanda ke cikin shawarar. A cewarsa, kayayyakin more rayuwa irinsu layin dogo, da hanyoyin mota, da tashoshin jiragen ruwa, suna da muhimmanci matuka ga nahiyar Afirka, domin za su iya taka muhimmiyar rawa a cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen dake nahiyar Afirka, ko kuma tsakaninsu da kasashen dake wajen nahiyar. Sannan, Ta hanyar kara gina kayayyakin, za a samu damar ciyar da tattalin arzikin kasashen Afirka gaba.

Ban da haka kuma, shugaba Kenyatta ya ambaci sabon layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi, wanda za a fara amfani da shi nan ba da jimawa ba. A cewarsa, kamfanin CRBC na kasar Sin ne ya dauki nauyin gina layin dogon da ya tashi daga birnin Mombasa dake bakin tekun kasar Kenya, sa'an nan ya isa Nairobi, hedkwatar mulkin kasar. Shugaban ya ce, wannan layin dogon zai taimakawa kasar Kenya ta fuskar raya tattalin arziki, da rage talauci, da samar da guraben aikin yi, gami da rage kudin da ake kashewa domin jigilar kayayyaki.

Haka zalika, za a iya kafa wasu ma'aikatu dab da layin dogon, domin samar da ayyukan yi ga mutanen da ke zama cikin kangin talauci, yana mai cewa, hakan zai kawo sauyi ga yanayi da suke ciki.

Har wa yau kuma, shugaban ya ce, alfanun da layin dogon zai haifar ba kasar Kenya kadai zai shafa ba, domin zai yi amfani wajen taimakawa yankin gabashin nahiyar Afirka bude kofarsa, da yin gyare-gyare ga tsarin tattalin arzikinsa, tare da samar da dimbin damammaki ga jama'ar nahiyar Afirka. Ya bayyana fatansa na ganin kasar Sin ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka, musamman ma a fannin kara tsawon layin dogon, ta yadda zai hada sauran kasashen dake gabashin Afirka irinsu Uganda da Ruwanda. Sa'an nan a karshe, layin dogon ya hada kasashen Afirka da nahiyar Asiya. Ta wannan hanya, za a bude wa nahiyar Afirka wata hanyar samun jari daga ketare, da kara saurin ci gaban tattalin arzikinta.

A cewar shugaba Kenyatta, karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", kasar Sin da kasashen Afirka za su iya hadin gwiwa, musamman ma a fannoni guda 2.

Na farko shi ne sanya kasar Kenya da sauran kasashen dake gabashin nahiyar Afirka su kara sayar da kayayyakinsu a kasar Sin. Na biyu kuwa shi ne, barin kasar Sin ta kara bude ma'aikatu a nahiyar Afirka, ta yadda za a samar da karin guraben ayyukan yi ga matasan nahiyar.

Ban da wannan kuma, Uhuru Kenyatta ya tabo maganar mu'ammalar dake tsakanin Kenya da Sin a fannin al'adu, inda ya ce, jama'ar kasashen 2 sun dade suna kokarin mu'ammala da juna, la'akari da yadda jiragen ruwan kasar Sin ke isa Malindin dake bakin tekun kasar Kenya kafin shekaru 600 da suka wuce.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China