170512-wakilin-habasha-dake-mdd-shawarar-ziri-daya-da-hanya-daya-ta-biya-bukatun-ci-gaban-duniya.m4a
|
A Laraba 10 ga wata ne, zaunannen wakilin kasar Habasha dake MDD Tekeda Alemu ya gaya wa manema labarai a birnin New York na kasar Amurka cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta biya bukatun ci gaban kasashen duniya, duk da cewa kasar Sin ce ta bullo da shawarar, amma tana shafar muradun daukacin kasashen duniya, saboda shawarar ta jaddada cewa, yana muhimmanci a samu ci gaba tare bisa tushen adalci da moriyar juna.
Yayin da zaunannen wakilin Habasha dake MDD Tekeda Alemu ya zanta da manema labarai na kafofin watsa labarai na Sinanci a birnin New York, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, yana komawa baya a kai a kai, a karkashin irin wannan yanayi, kasar Sin ta bullo da shawarar "ziri daya da hanya daya", hakan ya kawo sabon kaimi ga ci gaban duniya, ana iya cewa, shawarar ta biya bukatun ci gaban duniya. Alemu yana mai cewa, "An bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya' a daidai lokacin da ya dace, yanzu al'ummomin wasu kasashen duniya suna kyamar baki, ana kuma nuna bambanci ga mutanen dake wurare daban daban, kana ba a samu daidaito ba yayin da ake kokarin raya tattalin arziki a yankunan fadin duniya. A saboda haka muna bukatar samun wata dabara domin hada kan al'ummomin kasashen duniya, ta yadda za su iya yin hadin gwiwa ba tare da kawo wata baraka ba. Shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta bullo da ita ta samar mana damar kara karfafa hadin gwiwa da cudanya a tsakanin kasa da kasa da shiyya da shiyya da kuma tsakanin al'ummomin kasashen duniya. Shi ya sa ina ganin cewa, shawarar ta biya bukatun ci gaban duniya."
Alemu ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samu karbuwa matuka a wajen al'ummomin kasashen fadin duniya, shi ne domin shawarar ta fi dora muhimmanci kan adalci da moriyar juna, yana mai cewa, "Abu mafi muhimmanci shi ne shawarar 'ziri daya da hanya daya' tana maraba da daukacin kasashen duniya da su zo a dama da su, kana shawarar ta fi mai da hankali kan adalci da moriyar juna, hakan ya fi dacewa da burin samun ci gaba tare na yawancin al'ummomin kasashen duniya."
Alemu ya bayyana cewa, domin nuna goyon baya ga shawarar "ziri daya da hanya daya", an zartas da wasu kudurori a yayin babban taron MDD da kuma taron kwamitin tsaron MDD, hakan ya gaskata cewa, shawarar tana da babbar ma'ana. A sa'i daya kuma, shawarar tana da nata burin kamar na muradun tabbatar da dauwanammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2030, misali wasu ayyukan dake karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" za su taimakawa kasashe masu tasowa kamar Habasha su kara karfinsu na samun ci gaba bisa dogaro da kansu, wato za su iya kama kifi da kansu, amma ba wai su jira a ba su kifi ba, hakan shi ma zai taimaka wajen cimma burin tabbatar da muradun MDD.
Alemu ya ce, "Shawarar 'ziri daya da hanya daya' tana da babbar ma'ana wajen tabbatar da muradun MDD nan da shekarar 2030, saboda idan kasashe suna son shiga aikin tabbatar da muradun, dole ne su samar da albarkatu da dama a fannoni daban daban, amma yanzu wasu kasashen suna fama da karancin albarkatun da ake bukata, a wannan lokaci kuma, kasar Sin ta bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya' wadda za ta kawo sabbin albarkatu da jari da fasahohi da kasashen da suke bukatar shiga ba dama da su, shi ya sa ana iya cewa, shawarar za ta taimakawa muradun MDD."
Alemu ya ci gaba da cewa, yanzu a wasu kasashe masu tasowa na nahiyar Afirka, har yanzu babu manyan kayayyakin more rayuwar jama'a irin na zamani, lamarin da ya kawo illa ga ci gaban kasashen, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kawo musu sabbin damammakin hadin gwiwa da cudanya da kuma samun ci gaba.
Alemu ya ce, layin dogon da kewaye birnin Addis Ababa da kamfanin kasar Sin ya gina yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar ta Habasha. Kana ya jinjinawa huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Habasha a cikin 'yan shekarun da suka gabata, inda ya bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta bude wani sabon babi ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Yana mai cewa, "Huldar dake tsakanin Sin da Habasha tana gudana yadda ya kamata, kuma Habasha ta samu babban ci gaba cikin shekaru kusan ashirin da suka gabata sakamakon hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, yanzu ko shakka babu sauran kasashen Afirka za su samu moriya daga wannan shawarar ."
Alemu ya jaddada cewa, ba ma kawai shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta kawo moriya ga kasashe masu tasowa kawai ba, har ma za ta samar da damammaki ga kasashe masu ci gaba a Asiya da Turai da Afirka domin su samu ci gaba tare da kasashe masu tasowa ta hanyar yin hadin gwiwa, yana ganin cewa, shawarar tana da babbar ma'ana ga daukacin kasashen duniya.(Jamila)