in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nan gaba kadan layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya zai dawo hayyacinsa
2017-05-03 13:34:13 cri

Idan muka yi waiwaye, za mu gano cewa, an shimfida layin dogon da ya hada kasashen Tanzaniya da Zambiya a lokacin da ake kokarin 'yantar da al'umma a kudancin nahiyar Afirka. Amma bayan shafe dogon lokaci, a wani irin yanayin da layin dogon ke ciki a halin yanzu?

Mwanyika, wani tsohon ma'aikacin layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya, wanda ya yi shekaru 41 yana aiki. Tun daga shekarar 1976 zuwa 1986, ya yi aikin tukin jirgin kasa har na tsawon shekaru 10. Ya bayyana cewa:

"Lokacin da nake tuka jirgin kasa, akwai jiragen kasa guda 12 da su kan yi zirga-zirga a kowace rana."

Amma a halin yanzu, jiragen dakon kaya biyu ko hudu ne kadai ke zirga-zirga a kan wannan layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya, hatta albashin da Mista Mwanyika ke samu a halin yanzu ya bambanta kwarai da na shekarun baya. Ya ce, da ya zama matukin jirgin kasa, kowa na alfahari da shi. Amma tun bayan da ya yi ritaya a bara, kawo yanzu, bai samu komai daga fanshonsa ba.

"Ban san nawa ne kudin fanshona ba a kowane wata, saboda tun da na yi ritaya daga aiki a bara, ban samu ko sisin kwabo ba. Hukumar kula da harkokin layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya ba ta da kudi."

Babu tantama, a halin yanzu dai, wannan layin dogo, wanda kasar Sin ta bada taimakon ginawa yau da shekaru sama da 40 da suka shige, ba ya aiki yadda ya kamata.

Alal misali, daga shekarar 2015 zuwa 2016, kayan ton dubu 130 ne kawai aka yi jigilarsu ta hanyar jirgin kasa daga Tanzaniya zuwa Zambiya, sabanin yadda a baya adadin ya taba kai wa kusan ton miliyan 1.3.

A nasa bangaren, babban manajan hukumar kula da harkokin layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya, Bruno Ching'andu ya yi bayanin cewa, raguwar yawan kayan da a kan yi jigilarsu ne babban dalilin da ya jefa wannan layin dogo cikin mawuyacin hali. Inda ya ce :

"Bayan shimfida wannan layin dogo, da can baya, kasar Zambiya ba ta iya amfani da tashoshin jiragen ruwa a kudancin Afirka, kuma a lokacin Dar es Salaam shi ne mashigin teku daya tilo da ake iya amfani da shi. Shi ya sa a wannan lokaci, ana amfani da layin dogon da ya tashi daga Tanzaniya zuwa Zambiya kwarai domin jigilar kaya. Amma daga bisani, bayan kawo karshen nuna wariyar launin fata a wasu kasashen kudancin Afirka, sai aka fara amfani da tashohin jiragen ruwa na sauran kasashe."

Mista Bruno ya ci gaba da cewa, sai dai kuma, bayan wadannan canje-canje, ba'a yi garambawul ga layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya ba. Yana mai cewa:

"Ba mu tunkari wadannan sauye-sauye a kan lokaci ba. Sannu a hankali, sai harkokinmu na jigilar kaya ya samu koma-baya, kana ba mu da isassun kudi na tafiyar da ayyukanmu. A karshe, ba mu iya gamsar da fasinjoji, abun da ya sa su zabar sauran hanyoyin sufuri."

Kamar yadda muka ambato a baya, kasar Sin ta bada taimako da tallafi wajen shimfida wannan layin dogo daga Tanzaniya zuwa Zambiya. Miao Zhong, shi ne shugaban rukunin kwararru dake aiki a wannan layin dogo, inda ya yi shekaru sama da goma yana aiki. Bayan da kasashen Tanzaniya da Zambiya suka karbi aiki na tafiyar da wannan layin dogo, kasar Sin ta fara bada hadin-kai wajen samar da tallafin fasaha. Mista Miao Zhong ya ce:

"Duk lokacin da muke ba su hadin-kai ta fuskar fasaha, muna samar musu da jiragen kasa, da motoci da sauran wasu na'urorin aiki, a wani kokari na goyon-bayan harkokin layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya."

Ko da yake ana fuskantr kalubale da dama, amma ana sa ran za'a farfado da wannan layin dogo a nan gaba. A nasa bangaren, babban manajan hukumar kula da harkokin layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya, Bruno Ching'andu ya bayyana wasu shirye-shirye na raya wannan layin dogo, amma a ganin Miao Zhong, duk abubuwan da zai yi, kananan gyare-gyare ne kawai, yana mai cewa, in dai ana son farfado da layin dogon, ya zama dole a kara zuba jari a wannan fannin.

Mista Miao Zhong ya ce:

"A halin yanzu, muna cikin mataki na 16 na tallafawa layin dogon ta fuskar fasaha, za mu yi kokarin tabbatar da cewa, layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya zai yi aiki yadda ya kamata, da yin jigilar fasinjoji da kaya ba tare da ya fuskanci matsalar tsaro ba. A nan gaba kuma, akwai yiwuwa kasar Sin ta kara zuba jari a wannan layin dogo domin aiwatar da sauye-sauye da garambawul, ta yadda zai dawo hayyacinsa nan bada jimawa ba." (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China