170515-An-yi-taron-shugabannin-dandalin-tattaunawa-na-hadin-gwiwar-kasa-da-kasa-kan-ziri-daya-hanya-daya-a-Beijing-Murtala.m4a
|
A cikin muhimmin jawabin da shugaba Xi ya gabatar, ya bayyana cewa, ya bullo da wannan shawara ne sakamakon la'akari da halin da ake ciki yanzu a fadin duniya, inda ya ce:
"Yanzu kasashen duniya na kara dogaro da juna, kana ana kara fuskantar kalubaloli iri-iri a duniya, babu wata kasa da za ta dogara da kanta ita kadai. Ya zama dole kasashe daban-daban su yi mu'amalar manufofinsu, da yin hadin-gwiwa ta fannin tattalin arziki da neman bunkasuwa, ta yadda za su zama tsintsiya madaurinki daya, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya."
Xi ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa su kara cudanya da juna tare da bude kofa ga juna, da yin koyi daga juna, domin neman samun bunkasuwa kafada da kafada. Xi ya bayyana cewa:
"Shawarar 'ziri daya hanya daya' ta samo asali daga kasar Sin, amma shawara ce ta kowa da kowa. Wannan shawara ta shafi yankuna, da al'adu daban-daban, wanda ya zama wani dandalin hadin-gwiwa dake bude kofa ga kowace kasa. Wannan shawara ta 'ziri daya hanya daya' tana maida hankali kan nahiyoyin Asiya da Turai, amma kofarta a bude take ga duk kasar dake son shiga."
Xi Jinping ya ce, yana farin-cikin ganin cewa, wannan shawara ta samu dimbin goyon-baya daga gamayyar kasa da kasa, yana kuma fatan dandalin tattaunawar da aka yi a wannan karo, zai taimaka ga kara cimma matsaya daya, da bullo da wata alkibla ga shawarar "ziri daya hanya daya".
Xi ya bada shawarar cewa:
"Muddin ana son samun nasarar aiwatar da shawarar 'ziri daya hanya daya', to ya zama tilas a zage damtse. Ya kamata a yi kokarin inganta shimfida layukan dogo da hanyoyin mota, da kuma kara gina tashoshin ruwa a teku, da shimfida bututun jigilar mai da iskar gas da kuma wutar lantarki. A dayan bangaren kuma, dole ne a kara kokarin gina yankin cinikayya maras shinge, da kara samar da guraban ayyukan yi ga jama'a, da kara yin kirkire-kirkire."(Murtala Zhang)