in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD: Shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta nuna dabarar kasar Sin wajen sa kaimi ga ci gaban duniya
2017-05-10 13:45:55 cri

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai kawo wa kasar Sin ziyara daga ranar 13 zuwa ranar 15 ga wata, sa'an nan zai halarci taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya" wanda za a yi a birnin Beijing. Wannan ne karo na farko da Mr. Guterres zai kawo wa Sin ziyara tun bayan da ya hau kujerar magatakardan MDD.

Yayin da yake zantawa da manema labarai na kasar Sin a babbar hedkwatar majalisar a kwanan nan, ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta nuna dabarar kasar Sin wajen sa kaimi ga ci gaban duniya, wadda ta bayar da muhimmiyar gudummawa wajen daidaita matsalolin duniya, gami da sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa.

Yayin da magatakardan MDD Antonio Guterres ke zantawa da manema labarai na kasar Sin, ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar ta nuna dabarar kasar Sin wajen sa kaimi ga ci gaban duniya. Yana farin ciki da samun damar halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya".

Ya kara da cewa, taron kolin zai samar da wani dandali wajen karawa kowa fahimta game da shawarar "Ziri daya da hanya daya"

"A yayin wannan taron koli, mahalarta taron za su kara fahimtar dukkan ayyukan da ake gudanarwa bisa shawarar 'Ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta gabatar. Wadannan ayyuka, musamman ma ayyukan more rayuwar jama'a za su yi tasiri sosai wajen inganta sadarwa da cudanya tsakanin kasa da kasa. A waje daya kuma, taron kolin zai bai wa mahalartansa damar tattaunawa kan yadda za a yada amfanin shawarar yadda ya kamata, a kokarin kara azama wajen samun dauwamammen ci gaban duniya da zai samu karbuwa ga kowa."

A yayin zantawar, Mr. Guterres ya ambaci shakkun da ake yi wa batun ci gaban duniya da na ciniki a duniya cikin 'yanci. Kuma ya jaddada cewa, kasar Sin ta zabi wannan lokaci wajen kiran taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", lamarin zai karfafa zukatan kasa da kasa game da ci gaban duniya. Kuma bisa shawarar, dimbin mutane za su fahimci cewa, batun ci gaban duniya zai amfana wa kowa da kowa.

"Yanzu dimbin mutane na nuna shakku kan ci gaban duniya da yin ciniki a duniya cikin 'yanci, a ganinsu, dimbin mutane ba su iya cin gajiya daga ci gaban duniya. Sabo da haka ne, muke ganin ya kamata a gaggauta ba jama'ar kasashe daban daban kwarin gwiwar cewa, za a iya samun wata kyakkyawar hanya ta neman ci gaban duniya, sannan yin ciniki cikin 'yanci ma zai amfana wa kowa da kowa. Taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar 'Ziri daya da hanya daya' shi ne zai samar da irin wannan dandali da ma zarafi mai kyau."

Bugu da kari, Mr. Guterres ya nuna cewa, aikin aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" zai ingiza aikin cimma burin MDD na samun dauwamammen ci gaban duniya ya zuwa shekarar 2030, duk wadannan biyu sun kasance kyawawan hanyoyi na warware matsalolin da ke gaban duniya a yanzu.

"Ajandar neman samun dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030 ta MDD wata kyakkyawar hanya ce da za ta iya tinkarar kalubalolin duniya, wanda ya samu amincewar kowa. A waje da ya kuma, shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ita ma za ta taimaka wajen cimma wannan burin, ta yadda za ta tallafa wa dimbin kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa wajen haye wahalhalu don samun ci gaba. Manufofin shawarar 'Ziri daya da hanya daya' da na Ajandar neman samun dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030 ta MDD iri daya ne. Ayyukan more rayuwar jama'a da ake gudanarwa bisa shawarar za su kyautata cudanya da sadarwa a tsakanin yankuna daban daban da ma jama'ar yankuna daban daban, baya ga gaggauta ci gaban cinikayya, duk wadannan za su sa kaimi ga cimma burin samun dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030."

Haka zakila Mr. Guterres ya furta cewa, hukumomin MDD za su ci gaba da tallafawa ayyukan da za a gudanar bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin inganta aikin aiwatar da shawarar.

"Da farko dai, hukumomin MDD za su taimaka wa kasashen da shawarar ta shafa wajen karbar wadannan sabbin ayyukan hadin kai, da ba su kwarin gwiwar shigar da shawarwarin cikin hanyoyin da suke bi na samun ci gaban, domin ingiza aiwatar da shawarar yayin da suke samun ci gaban mai dorewa. Ban da wannan kuma, shawarar da kuma ayyukan hadin kai da abin ya shafa za su taimaka wa muhimman batutuwan da MDD ke mai da hankali a kan su, kamar shirin 'hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa'. Bugu da kari, nasarorin da kasar Sin ke samu yayin da take samun ci gaban, za su zama abin koyi ga dimbin kasashe maso tasowa."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China