170514-An-bude-babban-taron-dandalin-tattaunawa-na-hadin-gwiwar-kasa-da-kasa-kan-ziri-daya-hanya-daya-a-Beijing-Murtala.m4a
|
A cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron, ya ambaci babban dalilin da ya sa kasar Sin ta bullo da wannan shawara ta "ziri daya hanya daya" a shekaru hudu da suka gabata, inda ya ce:
"Duniyarmu tana fuskantar kalubale iri-iri. Ya kamata mu sanya sabon kuzari wajen habaka tattalin arzikin duniya, da samar da daidaito wajen neman bunkasuwa, har ma da rage gibin dake kasancewa tsakanin mawadata da matalauta. Ana fama da tashin hankali da yaduwar ayyukan ta'addanci a wasu sassan duniya. A lokacin kaka na shekara ta 2013, a kasashen Kazakhstan da Indonesiya, na gabatar da wasu shawarwari guda biyu, da suka hada da, gina zirin tattalin arziki ta hanyar siliki, gami da raya hanyar siliki kan teku a karni na 21, wato shawarar 'ziri daya hanya daya'".
A halin yanzu, akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 100 da suke amsa kirar wannan shawara ta 'ziri daya hanya daya', hatta ma akwai kasashe da kungiyoyi sama da 40 wadanda suka rattaba hannu tare da kasar Sin kan yarjeniyoyin hadin-gwiwa a wannan fanni.
A wannan karon, shugabannin dukkan kasashe uku da suka kafa kawancen tattalin arzikin kasashen Turai da Asiya, sun halarci taron, ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin, da shugaban Kazakhstan Nazarbayev, gami da shugaban Belarus Alexander Lukashenko. A nasa jawabin, shugaban Rasha Vladimir Putin ya nuna kyakkyawan fatansa game da makomar shawarar "ziri daya hanya daya", inda ya ce:
"Wannan shawara ta samar da damammaki ga hadin-gwiwar kasashen Turai da na Asiya, muna matukar goyon-bayan wannan shawara. Muna da imanin cewa, kawancen tattalin arzikin kasashen Turai da Asiya, da wannan shawara ta 'ziri daya hanya daya', za su taimaka sosai ga dunkulewar nahiyoyin Turai da Asiya baki daya a nan gaba."
Daga shekara ta 2013 zuwa yanzu, yayin da kasar Sin ke kokarin yayata wannan shawara ta "ziri daya hanya daya", ta jaddada muhimmancin yin hadin-gwiwa dake kawowa juna moriya, wato kasashe daban-daban za su ci gajiya daga wannan shawara, ba kasar Sin ita kadai ba.
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana ra'ayinsa dake cewa:
"Shawarar 'ziri daya hanya daya' ta samo asali ne daga tarihi, yanzu kasar Sin ta zama babbar jagora a harkokin kasa da kasa. Kasar Sin ta taba bullo da wasu muhimman shawarwari, ciki har da kafa bankin zuba jarin manyan ababen more rayuwa na nahiyar Asiya. Wannan shawara ta 'ziri daya hanya daya' ita ce wani sabon salo na tsohuwar hanyar siliki a lokacin da, ya kamata mu kara raya shi da sanya sabon jini a ciki, domin samar da moriya ga duniya baki daya. Majalisar Dinkin Duniya a shirye take wajen yin wannan aiki, ta yadda za'a samar da ci gaba mai dorewa, har ma kowa zai iya cin alfanu."
A dayan bangaren kuma, akwai wasu mutanen da suka nuna shakku game da wannan shawara ta "ziri daya hanya daya" da kasar Sin ta bullo da ita. Game da damuwarsu, a cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya sake nanata muhimmancin yin hadin-gwiwa dake kawo moriya ga kowace kasa. Mista Xi ya ce:
"Kasar Sin na son nunawa kasashen duniya yadda ta samu nasara wajen samun ci gaba, amma sam ba za ta yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ba, kuma ba za ta tilasta wata kasa don ta bi tsarin zamantakewar al'ummarta da tsarin bunkasuwarta na kasar Sin ba. Za'a kaddamar da wani sabon salo na neman samun moriya tare, yayin da kasar Sin ke kokarin yayata shawarar 'ziri daya hanya daya'. Duk inda wata kasa take, ko Asiya, ko Turai, ko Afirka, ko sauran yankuna, za ta iya yin hadin-gwiwa tare da kasar Sin don raya 'ziri daya hanya daya'. Dukkan kasashe za su iya cin gajiya daga wannan shawara."(Murtala Zhang)