in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin gyara layin dogo dake hade kasashen Tanzania da Zambiya zai kawo karin damar bunkasa yankin tattalin arzikin Zambiya
2017-04-25 11:03:34 cri

Yanzu haka ana tattaunawa kan yadda za a gyara, da kuma kyautata yanayin layin dogo dake hade kasashen Tanzania da Zambiya a tsakanin kasashen Sin da Zambiya da Tanzania. A wani yankin dake kusa da tashar karshe ta wannan layin dogo a kasar Zambiya, akwai wata shiyyar Chambishi, ta yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci da kasashen Zambiya da kasar Sin suka kafa. Sakamakon fuskantar matsaloli iri daban daban, layin dogo na Tanzania da Zambiya bai taka rawa kamar yadda ya kamata ba kan yankin da ake fata. Amma idan an gyara da kuma kyautata yanayin wannan layin dogo, tabbas zai taka muhimmiyar rawa ga wannan yanki na bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci.

A cikin yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci na Chambishi, wanda fadinsa ya kai murabba'in kilomita 11, kuma aka kafa shi a zirin ma'adinan tagulla, yanzu haka ana iya gina dakunan masana'antu iri iri. A cikin wani dakin rarraba ma'adinai, Mr. Gong Linmao, mataimakin sashen kula da harkokin yau da kullum na sashen Afirka a kamfanin NFC ya gaya wa wakilinmu cewa, "Wannan na'urar nika ma'adanai ce. Ana zuba garin ma'adinai a cikin na'urar. Bayan da na'urar ta nika su, za su zama kayayyakin da ake bukata."

Mr. Gong Linmao ya bayyana cewa, yawan tagulla dake cikin duwatsen da aka haka bai wuce kashi 2 cikin dari kacal ba. Bayan da aka zaba da kuma tace duwatsen, za a iya samun danyar tagulla, wadda yawan tagulla ta kan kai kashi 98 cikin dari.

Mr. Deng Yun, mataimakin direktan kamfanin tace sinadarin tagulla na Chambishi ya bayyana cewa, yawan danyar tagulla da kamfaninsa ke samarwa ya kan kai ton dubu 200, kuma ana fitar da su zuwa kasar Sin. Mr. Deng Yun y ace, "Wannan kamfani ne mafi girma da kasar Sin ta zuba jari a ketare cikin sa. A da, a lokacin da babu wannan kamfani na tace sinadarin tagulla, a kan yi jigilar duwatsun tagulla zuwa kasar Sin. Yanzu ana da wannan kamfani, baya ga samun karin darajar tagulla, ana kuma iya samar da karin guraban aikin yi ga mazauna kasar Zambiya."

Amma har yanzu wani abin bakin ciki shi ne, ana amfani da motoci ne wajen sufurin wadannan tagulla ton dubu 200 zuwa kasar Sin a kowace shekarar, wato ana bukatar kudin mai tarin yawa wajen yin sufurinsu, maimakon layin dogo wanda za a iya tsimin kudin zirga-zirga. A hakika dai, ana da kilomita dari 2 ne kacal tsakanin tashar karshe ta layin dogo na Tanzania da Zambiya, da yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya na Chimbishi. Bugu da kari, wannan yanki yana kusa da layin dogo na kasar Zambiya. Ma'aikatan yankin su kan ce, "A lokacin da muke barci, muna jin karar jiragen kasa." Tun da haka ne, me ya sa har yanzu ba a fara amfani da jiragen kasa wajen jigilar kayayyakin tagullar ba? Mr. Deng Yun ya kara da cewa, "An dade ba a gyara layin dogo na Tanzania da Zambiya ba. Kusan ba a iya kulawa da shi kamar yadda ya kamata ba. Bugu da kari, a kan sace kayayyakin wannan layin dogo."

Ban da matsalar rashin kulawa, idan ba a iya yin jigilar kayayyaki a kan lokaci, wannan wata babbar matsala ce ga kasuwanci. Sabo da haka, yanzu ana fitar da tagullan kasar Zambiya zuwa kasar Sin a tasoshin ruwa na kasashen Tanzania, da kasar Afirka ta kudu, da Namibiya, da Mozambique. Amma bayan da aka fitar da shirin gyara da kuma kyautata yanayin layin dogo na Tanzania da Zambiya, an sake mai da hankali kan wannan layin dogo. Mr. Zan Baosen, babban direktan yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci na Zambiya da Sin yana gani cewa, wannan shiri wani albishiri ne ga yankinsa. Ya nuna cewa, "Idan an yi kididdiga, za a gane cewa, ana kashe makudan kudade wajen jigilar kayayyakin kasar Zambiya. Idan an rage yawan kudin jigilar kaya, tabbas ne hakan zai haifar da kyakkyawan tasiri ga aikinmu na shigar da jari a yankin mu. Bugu da kari, za a iya kara karfin yin takara a kasar Zambiya ta hanyar shigar da 'yan kasuwa da masu zuba jari a kasar, ta yadda za a iya bunkasa masana'antun sarrafa kayayyaki a kasar."

Zan Baosen ya kara da cewa, idan sabon layin dogo na Tanzania da Zambiya zai iya biyan bukatun da yankin bunkasa tattalin arziki da cinikayya cikin 'yanci yake da su, tabbas zai ba da gudummawa ga kokarin gudanarwa, da kuma bunkasa layin dogo na Tanzania da Zambiya kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China