in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in WIPO: Shirin "Ziri daya da hanya daya" salon hadin gwiwa ne mai inganci
2017-05-08 11:09:29 cri

Kwanakin baya babban jami'in hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya WIPO Francis Gurry ya zanta da wakilin gidan rediyon CRI kafin ya tashi zuwa nan birnin Beijing domin halartar dandalin hadin gwiwa game da shirin "Ziri daya da hanya daya", inda ya bayyana cewa, shirin wani nau'in hadin gwiwa ne mai inganci wanda zai kawo babbar moriya ga kasashen da abin ya shafa.

Francis Gurry ya hau kan kujerar babban jami'in hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya tun daga shekarar 2008, kawo yanzu yana rike da mulkinsa a hukumar a wa'adin aiki na biyu. Kan batun game da shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, Gurry yana ganin cewa, wannan shawarar tana da muhimmanci matuka, haka kuma dandalin da za a kaddamar a birnin Beijing game da shirin zai taka rawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Gurry yana mai cewa, "Dandalin da za a kaddamar yana da babbar ma'ana, saboda zai taimakawa aikin tabbatar da shirin 'Ziri daya da hanya daya', yayin dandalin, ba ma kawai ana iya tattaunawa kan kokarin da ake yi bane, har ma ana iya tsara shirin da zai dace a nan gaba, kana ana iya yin la'akari da batun game da yadda za a kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kungiyoyin kasa da kasa yayin da ake kokarin tabbatar da shirin. A saboda haka ina ganin cewa, dandalin yana da muhimmanci matuka, kuma an shirya shi ne a lokacin da ya dace."

Gurry yana ganin cewa, salon hadin gwiwa da shirin ya gabatar yana da inganci sosai, wato ya sha bamban da salon hadin gwiwa da aka tsara, bisa wannan shirin ne, an jaddada cewa, ya fi kyau a kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen da shirin ya shafa, daga baya kuma sai a fara gudanar da hadin gwiwar ciniki tsakanin su. Shi ya sa ana iya cewa, shirin ya gabatar da salon hadin gwiwa mai inganci, shi ma zai kara karfafa karfin yin hadin gwiwar ciniki na kasashe masu tasowa da shirin ya shafa.

Gurry ya kara da cewa, tsara tsarin kare ikon mallakar fasaha na duniya mai inganci zai taimakawa aikin kyautatuwar tsarin kare ikon mallakar fasaha na kasashen dake da nasaba da shirin "Ziri daya da hanya daya", tare kuma da samar da wani muhalli mai kyau domin yin kirkire-kirkire da kuma samun dauwamammen ci gaba. Hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya tana son shiga shirin nan, Gurry ya bayyana cewa, "Muna fatan za mu iya shiga shirin "Ziri daya da hanya daya", saboda muna ganin cewa, shirin nan zai kara karfafa hadin gwiwa a fannin kare ikon mallakar fasaha dake tsakanin kasa da kasa, mu ma muna son samar da wajibabbun goyon baya ga shirin a ko da yaushe."

Gurry ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin da kasashen duniya ke ciki yana haifar da manyan sauye-sauye, haka kuma tsarin yin hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa yana bukatar kyautatuwa, kana ya kasance bambanci wajen karfin fasaha da matsayin samun ci gaba dake tsakanin kasa da kasa, shi ya sa, ana gudanar da hadin gwiwa ta hanyoyi iri daban daban, yanzu dai, kasashen da suka shiga shirin "Ziri daya da hanya daya" suna gudanar da hadin gwiwa bisa amincewar juna a fannonin tarihi da harsuna da al'adu da sauran dalilai. Gurry yana mai cewa, "Idan an gudanar da hadin gwiwa bisa tushen amincewar juna a fannonin tarihi ko huldar ciniki, to, za a samu ci gaba cikin sauri, ina fatan sakamakon da aka samu zai taimakawa hadin gwiwar dake tsakanin bangarori da dama a fadin duniya, na amince da cewa, tabbas ne shirin 'Ziri daya da hanya daya' zai taka muhimmiyar rawa kan ci gaban kasashen da shirin ya shafa."

A watan Janairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "samar da makoma mai haske ga bil Adama" a hedkwatar MDD dake Geneva, Gurry ya jinjinawa jawabin, yana mai cewa, "Abun da shugaba Xi Jinping ya nunawa al'ummomin kasashen duniya a cikin wannan jawabi shine, kasar Sin tana fatan daukacin kasashen duniya za su samu cigaba tare, bisa tushen nunawa juna goyon baya da samun moriyar juna. Ina ganin cewa, wannan tunani ya kara karfafa zuciyar kowa da kowa, wanda kuma zai biya bukatun daukacin al'ummomin kasashen duniya baki daya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China