170515-Xi-Jinping-Ziri-daya-hanya-daya-Kande.m4a
|
Jiya Lahadi ranar 14 ga wata, an kaddamar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing. A daren ranan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shirya liyafa, don maraba da zuwan baki mahalarta taron daga kasashe daban daban. A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya hanya daya" ta kunshi burinmu na kara cudanya a tsakanin al'adu daban daban, da na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, da na neman ci gaba gaba daya, gami da na neman jin dadin zaman rayuwa. Muddin mu yi kokari tare, tabbas ne sha'aninmu zai amfana wa zuriyoyinmu kamar yadda hanyar siliki ta zamanin da.
An shirya liyafar dare a babban dakin taruwar jama'a a birnin Beijing jiya Lahadi ranar 14 ga wata. Da farko dai, shugaban kasar Sin Xi Jinping da matarsa Madam Peng Liyuan, sun yi marhabin da zuwan shugabannin tawagogin kasashen waje da matansu, da ke halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya hanya daya", daga baya kuma sun shiga dakin shirya liyafa baki daya.
Shugaba Xi Jinping ya ba da wani jawabi, wanda ya fara daga labarin birnin Beijing mai dogon tarihi, inda ya bayyana cewa, Beijing wani tsohon birni ne mai shekaru fiye da dubu daya, kana wani sabon birni ne na zamanin yanzu, wanda yake ta nuna sabon kyan surarta bisa ci gaban kasar Sin. Ban da wannan kuma, Beijing wani babban birni na kasa da kasa ne, inda ake iya samun cudanyar al'adun kasashe daban daban. Shugaba Xi ya kara da cewa,
"Mu Sinawa mu kan cewa, daga digon ruwa, ana iya gano yanayin teku, daga kwayar rairayi, ana iya gano duk duniya. A zamanin da, Beijing wani karamin gari ne, amma yanzu ya zama wani babban birni na kasa da kasa, wanda ya nuna mana cewa, mu bil Adam muna zama a gida bai daya, muna da kaddara bai daya. Ko da yaushe mu bil Adam muna ta samun bunkasuwa bisa hanyar kara cudanya, da samun fahimta a tsakanin kabilu daban daban da al'adu daban daban."
Bugu da kari, Xi Jinping ya nuna cewa, yau da shekaru fiye da dubu biyu, kakanin kakanin al'ummar Sin sun kafa hanyar siliki bisa burin kara dakon zumunci da cudanya, wadda ta bude wani sabon shafi ga cudanyar kasa da kasa a tarihin wayin kan bil Adam. A yau ma, ana tattaunawa kan samun ci gaba bisa shawarar "Ziri daya hanya daya", lamarin da ya kasance gadon da aka ci daga tarihi, gami da wani zabi mai dacewa wajen samar da makoma mai haske. Shawarar "Ziri daya hanya daya" ta kunshi burinmu na kara cudanya a tsakanin al'adu daban daban, da na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, da na neman ci gaba gaba daya, gami da na neman jin dadin zaman rayuwa. Shugaba Xi yana mai cewa,
"Shawarar 'Ziri daya hanya daya', ta kunshi burinmu na neman samun bunkasuwa gaba daya, wadda za ta taimaka wa kasashe daban daban wajen warware matsalolin da ke gabansu, yayin da suke kokarin samun ci gabansu. Kana za ta ba da tasiri wajen rage gibin ci gaba a tsakanin kasa da kasa, da more sakamakon bunkasuwa, a kokarin raya wata makomar samun ci gaba bai daya, wadda za a iya jin dadi da shan wahala gaba daya. Haka zakila ma, shawarar 'Ziri daya hanya daya' ta kunshi burinmu na neman jin dadin zaman rayuwa, wadda za ta kokarta cimma burin ko wace kasa da ko wane jama'a, ta yadda jama'a za su iya jin dadin zamansu yadda ya kamata."
Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya furta cewa, za a tsara shirin hadin gwiwa bisa shawarar 'Ziri daya hanya daya' a yayin taron kolin da za a kira a ranar 15 ga wata. Yanzu ana tsayawa kan wani sabon mafari don kama wata sabuwar hanyar ci gaba. Xi ya bayyana cewa,
"Yanzu muna kan wata hanya mai cike da fatan alheri. Ina da imanin cewa, muddin mun yi kokari cikin hadin kanmu, ba tare da ja da baya da ma dakatar da takenmu, tabbas ne za mu samu wata makoma mai kyau da za ta amfani kowa da kowa. Haka kuma ina da imanin cewa, zuriyoyinmu za su ci gajiya sosai daga sha'aninmu na yanzu, kamar yadda tsohuwar hanyar siliki ta yi a zamanin da."
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da na Kazakhstan Nursultan Abishevich Nazarbayev da dai sauran shugabannin kasashe daban daban fiye da 700, sun halarci liyafar daren.(Kande Gao)