in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan kamfanonin Sin sun ba shirin "Ziri daya da hanya daya" muhimmanci
2017-05-09 14:01:37 cri

Tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", manyan kamfanonin kasar wadanda ke karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar suka ba shirin muhimmanci matuka, inda har suka ba da gudummowarsu ga aikin aiwatar da shirin.

Jiya Litinin 8 ga wata, daraktan kwamitin kula da dukiyar kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Xiao Yaqing ya bayyana cewa, kawo yanzu, gaba daya manyan kamfanonin dake karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar 47 sun shiga a dama da su cikin ayyukan da suka shafi shirin "Ziri daya da hanya daya".

Misali a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da sufurin jiragen kasa, da samar da wutar lantarki da dai sauransu, ana iya cewa, kokarin da ake ya sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin yankunan dake da nasaba da shirin nan na "Ziri daya da hanya daya".

Tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shirin a shekarar 2013, cikin gaggawa manyan kamfanonin dake karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar suka dora muhimmanci sosai kan ayyukan da rassan kamfanoninsu ke yi a kasashen ketare wadanda suka shiga shirin "Ziri daya da hanya daya".

Wadannan kamfanonin da yawansu ya kai 47 sun hada gwiwa da kamfanonin kasashen da suka shiga shirin domin gudanar da ayyukan raya kasa da adadinsu ya kai 1676.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka kira jiya, daraktan kwamitin kula da dukiyar kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Xiao Yaqing ya bayyana cewa, ayyukan da ake gudanar da su yanzu ko aka kammala su sun sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'ummar yankunan da shirin ya shafa. Inda ya ce, "A fannin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, manyan kamfanonin dake karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar Sin sun ba da babbar gudummowarsu, misali, layin dogon dake tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar Kenya, da babbar hanyar mota ta Karakoram da ta hada birnin Kash na jihar Xinjiang ta kasar Sin da birnin Thakot na kasar Pakistan, dukkansu gajiya ce ta al'ummomin yankunan. Kana kayayyakin wayar sadarwar da aka gina kan teku ko kan kasa su ma sun taimakawa ci gaban harkokin sadarwa a yankunan cikin sauri."

A fannin hadin gwiwa a bangaren makamashi kuwa, manyan kamfanonin suna gudanar da ayyukan samar da mai ko gas sama da sittin a kasashe fiye da 20, ban da haka kuma, kamfanonin sun samar da fasahohi na zamani ga kamfanonin kasashen da suka shiga shirin "Ziri daya da hanya daya" domin daga matsayinsu wajen haka ma'addinai.

Ko shakka babu, kokarin da kamfanonin suke, ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin yankunan.

Yayin da ake kokarin tabbatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", manyan kamfanonin dake karkashin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar ta Sin sun kara gano cewa, idan ana son taimakawa ci gaban yankunan, ya zama wajibi a yada da sakamakon da aka samu tare da al'ummomin kasashen, game da wannan batun ne shugaban kamfanin CRRC mai kera jiragen kasan karkashin kasa Liu Hualong ya bayyana cewa, "Muna mai da hankali sosai kan shiga harkokin yankunan da muke gudanar da aiki, musamman ma bangarorin zaman rayuwa da raya al'adu, idan muka tattaunawa da mazauna yankunan, muna amfani da sakamakon da muka samu, ta yadda za mu iya cimma burin da muka tsara bisa shirin 'Ziri daya da hanya daya', haka kuma dole ne mu yi kokari tare da su domin samun ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'umma a yankunan."

A halin da ake ciki yanzu, adadin ma'aikatan dake aiki a rassan kamfanonin a kasashen ketare ya kai dubu 384, a cikinsu, adadin ma'aikatan da aka yi hayar su a wuraren da kamfanonin suke ya kai kaso 85 bisa dari, inda a wasu wurare, adadin ya kai kaso 90 bisa dari. Ban da haka kuma manyan kamfanonin kasar Sin su ma sun samar da taimako ga mazauna wuraren a fannonin ba da ilmi da raya al'adu da kiwon lafiya da sauransu.

Shugaban kamfanin mai da gas na kasar Sin Wang Dongjin ya ce, "Kamfaninmu ya samar da taimakon kudi ga dalibai kusan dubu daya a kasar Kazakhstan domin su zo nan kasar Sin yin karatu, a kasar Myama, kamfanin yana taimakawa ayyukan gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a 177, wadanda suka kunshe da makarantu 72, da asibitoci 30, da kayayyakin samar da wutar lantarki da ruwan sha, da hanyoyi da kadarkai."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China