in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar dogo ta SGR da ta tashi daga Mombasa-Nairobi za ta soma aiki a watan Yunin bana
2017-05-02 12:23:02 cri

Kasar Kenya muhimmiyar kasa ce a fannin hadin kai bisa manyan tsare-tsare dangane da shirin nan na "Ziri daya hanya daya" a tsakanin Sin da kasashen Afirka, Haka kuma tana daya daga cikin kasashen dake sahun gaba a fannin gwajin hadin kan samar da kayayyaki tsakanin Sin da kasashen Afirka. Hanyar dogo ta SGR hanya ce da ta hade Mombasa wato tashar jiragen ruwa mafi girma a gabashin Afirka, da Nairobi babban birnin kasar Kenya. Bayan kafuwar hanyar dogon za a samu sauye-sauye a garuruwan dake dab da ita.

Wannan hanya dogo ta SGR da aka soma ginawa a shekarar 2014, tsawonsa ya kai kilomita 472, wadda kamfanin CRBC na kasar Sin ke daukar nauyin ginawa da gudanar da harkokinta, kuma za ta soma aiki ne a watan Yuni na bana.

Garin Voi yana cikin karamar hukumar Taita Taveta dake kudu maso gabashin kasar Kenya, kana wani muhimmin gari ne dake kan hanyar dogo ta SGR, kana wurin yawon shakatawa mafi girma a kasar Kenya wato Tsavor National Park da ya ratsa shi.

A yayin da yake ambato tasirin da hanyar dogon za ta kawo wa garin Voi da wuraren dake kewayensa, mai aikin cudanya kan aikin hanyar dogon SGR na gwamnatin karamar hukumar Taita Taveta, mista Tyson E.M. Mberi, wanda yake zaune a Voi tun yana yarantaka, yana mai cewa,

"Voi wani gari ne na ma'aikata, amma yanayin sufuri a yankin ba shi da kyau, akwai manyan motocin dakon kaya masu tarin yawa dake bin hanyar dake tsakanin Mombasa da Nairobi, shi ya sa ake samun cunkoso da aukuwar hadurra a hanyar. Amma, idan hanyar dogo ta SGR ta soma aiki, za a samu saukin zirga-zirga daga nan zuwa can. Don haka, hanyar dogon za ta taka muhimmiyar rawa a wurin, ta hanyar kara samar da ayyuka da ingata tattalin arziki al'ummar yankin."

An kuma kafa sansanin sashen kula da aikin hanyar dogo ta SGR a garin Voi, tun daga watan Agusta na shekarar 2014, ma'aikatan sashen suka soma zama a Voi, ya zuwa yanzu an kusa soma aikin hanyar dogon, mataimakin manajan sashen mista You Hao ya ce, sauye-sauyen da aka samu a garuruwan dake dab da hanyar dogon, ciki har da Voi sun burge shi sosai:

"Garin Voi babbar tashar sufuri ce dake tsakanin Nairobi da Mombasa, daga nan kuma ana iya zuwan kasar Tanzania. Ban da wannan kuma, yana tsakiyar gabashi da yammacin wurin yawon shakatawa na kasa na Tsavor da. Bayan hanyar dogon ta soma aiki, za a samu ingantuwar sana'ar yawon shakatawa kwarai a nan, kana za a samu kyautattuwar sufuri da sana'ar jigilar kayayyaki da dai sauransu a duk wurin."

Game da tasirin da hanyar dogon ta SGR za ta kawo ga sana'ar yawon shakatawa, babban daraktan otel din namun daji na Voi, Augustine Mwanake ya bayyana cewa,

"Hanyar dogon za ta kasance kayan sufuri mafi dacewa wajen inganta yawon shakatawar wurin, za ta samar da saukin zirga-zirga ga masu yawon shakatawa da mazauna wurin, hakan zai inganta harkokin cinikayya a wuraren dake kewayen wurin. Tun bayan da aka soma gina hanyar dogon, mun ci gajiyar karbar baki, muna fatan bayan hanyar dogon ta soma aiki, za a kara inganta zaman rayuwar mazauna wuraren dake dab da ita."

Bisa kididdigar da aka yi an ce, a lokacin da za a kwashe ana gina hanyar dogo ta SGRr, aikin ya kawo matsakaicin karuwar GDP na kasar Kenya da ya kai kashi 1.5 cikin dari, a sa'i daya kuma an samar da guraban aikin yi da dama, sai dai a yayin da ake gudanar a aikin a garin Voi kawai, an yin hayar ma'aikatai daga mazauna wurin da yawansu ya wuce dubu biyar. Caleb Biong Omwange yana daya daga cikinsu, inda yanzu haka yake aiki a ofishin gwaji da aka kafa a Voi. Game da ma'unin kasar Sin da ake bi wajen gina hanyar dogon, ya bayyana cewa,

"Idan aka kwatanta ma'aunin da ake bi kan hanyar dogo ta SGR da na sauran ayyuka da na taba yi, gaskiya ina ganin cewa, ma'aunin kasar Sin ya fi amfani da kuma rage lokacin aiki, irin wannan ma'unin ya fi dacewa da kasashe masu tasowa, musamman ma a Afirka kuma a kasar Kenya. Muna fatan za a gudanar da ayyuka da dama bisa wannan ma'uni, saboda ya taimake mu wajen samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a bisa babbar fasaha a cikin gajeren lokaci." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China