in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin "ziri daya da hanya daya" na taimakawa ci gaban tattalin arzikin Afirka
2017-04-24 10:59:26 cri

A 'yan kwanakin baya, aka kaddamar da bikin fara aikin wani kamfanin samar da siminti da kamfanin kasar Sin zai gina a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda firayin ministan kasar Hailemariam Desalegn ya jinjinawa taimakon da kamfanin na kasar Sin ke baiwa kasarsa, wajen samar da siminti.

A halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da shirin "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, kuma kasar Sin tana kara samar da goyon baya ga kasashen Afirka a fannoni daban daban, musamman ma wajen samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, kuma tuni aka fara ganin sakamako mai faranta ran al'umma.

A kasar Kenya, wata hanyar dogo dake hada birnin Mombasa, tashar ruwa mafi girma a yankin gabashin Afirka da Nairobi, fadar mulkin kasar, za ta fara aiki a watan Yuni mai zuwa, wannan aiki ya kasance aikin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a mafi girma a kasar ta Kenya a cikin shekaru sama da hamsin da suka gabata. kamfanin kasar Sin ne ya gina wannan hanyar dogo.

Babban manajan kamfanin hanyar dogo na kasar Kenya Atanas Ma'ina yana ganin cewa, hanyar dogon ta Mombasa zuwa Nairobi, za ta taka muhimmiyar rawa a fannin ci gaban tattalin arzikin Kenya, musamman ma a fannonin aikin gona, da hakar ma'adanai, da kirar kayayyaki, da makamashi, da yawon bude ido da sauransu. Kana za ta samar da karin guraben aiki ga mazaunan garuruwan dake kusa da hanyar dogon.

A watan Oktoban shekarar bara, hanyar dogo ta zamani dake hada birnin Addis Ababa na Habasha da birnin Djibouti na kasar Djibouti ta fara aiki a hukumanci, wannan ita ce hanyar dogo ta farko mai ketare kasashe biyu da kamfanin kasar Sin ya gina, ta hanyar amfani da ma'aunin fasahar kasar Sin, da kayayyakin da kasar Sin ke samarwa. Yanzu haka ana iya jigilar kayayyaki tsakanin biranen biyu cikin sati goma, amma a baya dole ne a yi amfani da babbar motar dakon kayayyaki a tsaron lokaci da ka iya kaiwa kwanaki uku. Ana iya cewa, hanyar dogon tsakanin Addis Ababa da Djibouti ta rage adadin kudaden da ake kashewa kan jigilar da kayayyaki, tana kuma taimakawa ci gaban masana'antun kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya taba bayyanawa a yayin da ya halarci taron ministocin harkokin wajen rukunin G20 a birnin Bonn na kasar Jamus a watan Fabrairun bana da cewa, hanyar dogo da hanyar mota da ake ginawa a kasashen Afirka, karkashin taimakon kasar Sin dukkansu sun riga sun zarta kilomita dubu 5, kana gwamnatin kasar Sin tana samar da horaswa ga kwararrun kasashen Afirka, da adadin su ya kai fiye da dubu 160.

Kara karfafa gama kai da hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa cikin dogon lokaci, har kullum gwamnatin kasar ta Sin tana mai da hankali matuka kan aikin, inda a yanzu take gudanar da shirin "ziri daya da hanya daya", kuma kasar Sin tana kara nuna kwazo da himma domin kara samar da goyon baya da kuma taimako ga kasashen Afirka, domin su cimma burin tabbatar da dauwamammen ci gaba cikin dogon lokaci.

A fannin gina kayayyakin more rayuwar jama'a kuwa, kokarin da kasar Sin take ya fi samun yabo daga wajen al'ummomin kasashen Afirka.

Wani shahararren kwararre mai nazarin aikin zuba jari a kasashen Afirka yana ganin cewa, ba dukkan masu zuba jari a fadin duniya su kan kawo alheri ga al'ummomin nahiyar Afirka ba, amma kasar Sin ba haka take ba. Misali, hanyar dogon da kamfanin kasar Sin ya gina a Addis Ababa na Habasha ta canja zaman rayuwar mazauna birnin, ta kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Ya ci gaba da cewa, kasashe kalilan ne a fadin duniya ke fatan samar da irin wannan taimako a kasashen Afirka, saboda babban aiki ne mai cin kudi da dama, kuma akwai wuya a samu moriya daga irin wadannan ayyuka.

Kasar Djibouti karamar kasa ce, wadda ba ta samu ci gaban tattalin arziki ba a nahiyar Afrika, kuma ba ta da arzikin albarkatun halitta, a saboda haka ta kaddamar da wasu ayyuka domin kara samar da jarin waje, bisa alkaluman da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya samar, an ce, yanzu kasar Sin ta kasance kasa da ta fi samar da yawan jari a kasar ta Djibouti, a fannin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a.

Mai jagorancin aikin nazarin tattalin arzikin Afirka ya bayyana cewa, kasar Sin abokiyar ciniki ce mafi girma ga kasashen Afirka, kuma hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu ya kawo babban sauya ga Afirka a fannonin ciniki da zuba jari, da kuma samar da kayayyakin more rayuwar jama'a baki daya. Shirin "ziri daya da hanya daya" shi ma yana kawo babban alheri ga al'ummomin kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China