in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Kenya: shirin "Ziri daya da hanya daya" zai taka rawa ga ci gaban kasashen Afirka
2017-05-05 10:05:34 cri

Za a gudanar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shirin "Ziri daya da hanya daya" a tsakiyar watan Mayun da muke ciki a nan birnin Beijing, kafin wannan, daraktan cibiyar nazarin manufofin raya kasashen Afirka ta kasar Kenya Robert Kagiri ya zanta da wakilin gidan rediyonmu a birnin Nairobi, inda ya bayyana cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" ya samar da wata sabuwar dama ga hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, haka kuma dandalin da za a kaddamar zai kasance wani gaggarumin bikin da zai jawo hankalin al'ummomin kasashe a fadin duniya.

Daraktan cibiyar nazarin manufofin raya kasashen Afirka ta kasar Kenya Robert Kagiri yana ganin cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta bullo da shi yana da babbar ma'ana ga ci gaban kasashen Afirka, ko shakka babu zai amfanawa sassan da abin ya shafa, yana mai cewa, "Shirin 'Ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta bullo da shi yana da ma'ana matuka ga kasashen Afirka, dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin tana kara bude kofarta ga kasashen waje, kana tana kara inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasa da kasa, musamman ma tsakaninta da kasashen Afirka, kana bisa wannan shiri kasar Sin tana kokarin neman samun wata hanyar raya kasa tare da sauran kasashen duniya, misali a fannonin tattalin arziki da ciniki da kuma raya kasa."

A shekarar 2013 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", wanda ya samu maraba matuka daga bangarori daban daban. Daga wancan lokaci, zuwa yanzu, wato a cikin shekaru sama da uku da suka gabata, an samu babban sakamako bayan kokarin da ake, misali, hanyar dogon dake tsakanin Nairobi da Mombasa na Kenya za ta fara aiki a watan Yuni mai zuwa, wannan hanyar dogo ita ce sabuwar hanyar dogo ta farko da kasar ta Kenya ta gina a cikin shekaru dari daya da suka gabata, kuma za ta ba da babbar gudummowa a fannin sufuri a yankin gabashin Afirka. Yayin da ake gina wannan hanya, an yi amfani da kudade da fasahohi da ma'auni da kayayyaki da manufofin tafiyar da harkokin kamfanin gina hanya na kasar Sin, bayan da hanyar dogon ta fara aiki, za a ci gaba da tsawaita ta har zuwa sauran kasashen Afirka, a karshe dai, za a hada kasashen gabashin Afirka guda shida wato Kenya da Tanzaniya da Uganda da Ruwanda da Burundi da kuma Sudan ta Kudu da hanyar dogo. Kagiri yana ganin cewa, irin wannan aiki zai taimaka wajen bunkasa harkokin cinikin dake tsakanin kasashe daban daban na nahiyar Afirka. Yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, kasashen Afirka ba su samu ci gaba sosai ba a fannin gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, a saboda haka kayayyakin more rayuwar jama'ar da za a samar ta hanyar shirin 'Ziri daya da hanya daya' za su kara kyautata fannonin sufurin kasa da ruwa da kuma na sama a kasashen da abin ya shafa, hakan shi ma ya dace da manufar kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasa da kasa ta kasashen Afirka."

Kasashen Afirka suna dora muhimmanci matuka kan shirin "Ziri daya da hanya daya", ban da gina kayayyakin more rayuwar jama'a, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ita ma tana da muhimmanci a fannonin samar da aikin yi da ba da ilmi da samar da fasahohi da dai sauransu. Kagiri ya bayyana cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" zai taimaka ga ci gaban kasashen Afirka a cikin shekaru biyar masu zuwa.

A game da dandalin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa game da shirin "Ziri daya da hanya daya" da za a kaddamar a tsakiyar watan Mayun da muke ciki a nan birnin Beijing, Kagiri ya bayyana cewa, "Wannan dandalin yana da babbar ma'ana, saboda za a gudanar da shi ne ba tare da rufa rufa ba, ba ma kawai kasashen da suka fara gudanar da aikin dake da nasaba da shirin kamar Kenya za su halarta ba, har ma wasu kasashe kamar Madagascar wadanda ba su shiga shirin ba tukuna su ma za su halarci dandalin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China