A yau ne aka fara wani gagarumin bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kan yankin Tibet na kasar Sin mai cin gashin kansa, bikin da ke gudana a gaban fadar Potala da ke birnin Lhasa, fadar mulkin yankin.
A yayin bikin na yau, ana sa ran babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Yu Zhengsheng zai gabatar da jawabi.
A ranar 1 ga watan Satumban shekarar 1965 ne yankin Tibet mai gashin kansa na kasar Sin ya samu 'yancin cin gashin kansa, bayan kafa majalisar wakilan jama'ar yankin, da kuma ta kananan hukumomi ta hanyar gudanar da zabuka.(Ibrahim)