Jihar Tibet na kokarin aikin samar da ruwan sha
Jiya Laraba 29 ga wata, gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin mai cin gashin kanta ta kira wani taron raya aikin samar da ruwan sha a birnin Lhasa, inda ta bayyana cewa, cikin shekaru 3 ko 5 masu zuwa, jihar za ta yi amfani da albarkarun ruwanta wajen kafa masana'antun samar da ruwan sha da ya kai ton miliyan 5 a ko wace shekara, wanda zai lashe sama da yuan biliyan 40, ta yadda jihar za ta kafa wani muhimmin wurin samar da ruwan sha a kasar Sin. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku