Hong Lei a ganawarsa da manema labarai a madadin gwamnatin kasar Sin yace ba a yarda ba ta kowane hali ga wata kasa ta tsoma baki cikin al'amuran cikin gida kasar da ya shafi Tibet.
Wannan lafazin na shi ya biyo bayan yiwuwar ganawa ne tsakanin shugaban kasar Amurka Barrack Obama da Dalai Lama a ranar alhamis mai zuwa 5 ga wata domin karin kumallon safe.
Mr Hong yace abinda ya shafi Tibet ya shafi kasar Sin da harkokin cikin gidanta don haka Sin ke kira ga Amurka da ta tsaya a kan matsayinta game da Tibet da kuma warware abin da ya shafi hakan don amfanan dukkan bangarori tsakanin Sin da ita kanta Amurkan.