Mataimakin shugaban reshen Lhasa na bankin jama'ar kasar Sin Zhang Wei ya bayyana cewa, an riga an kafa cibiyoyin taimakawa 'yan yankin Tibet ta fuskar aikin hada-hadar kudi guda 2436 cikin shekaru hudu da suka gabata, lamarin da ya taimaka wajen fadada bada hidima a dukkanin garuruwan dake yankin Tibet.
Yankin Tibet dai ya sha bamban da sauran wurare kan aikin hada-hadar kudi saboda kudin ruwa na ba da rancen kudi a wannan yanki ya ragu da kaso 2 cikin dari bisa na sauran wuraren kasar Sin.
Matakin da aka dauka na bada hidima kan aikin hada-hadar kudi ga manoma da masu kiwo dabbobi, ya taimaka wajen sa kaimi ga bunkasuwar kauyukan yankin Tibet wajen zuba jari a fannoni daban-daban. (Amina)