in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samar da shirin ko ta kwana na kasar domin yaki da bala'in gocewar kasa da ya faru a yankin Tibet
2013-03-30 16:29:31 cri
Hukumar kula da harkokin jama'ar kasar Sin ta bayyanawa 'yan jarida a ranar 30 ga wata cewa, hukumar da kuma kwamitin shawo kan aukuwar hadura daga indallahi na kasar sun samar da agajin gaggawa da karfe 10 na daren ranar 29 ga wata bayan aukuwar gocewar kasa da ya faru a garin Mozhukunggar na yankin Tibet. A halin yanzu, hukumar bada agajin wacce ta kunshi ma'aikatan hukumar kula da harkokin jama'ar kasar da kwamitin yaki da aukuwar hadura da kuma ma'aikatar harkokin albarkatun kasa sun isa yankin da lamarin ya auku, don yin bincike da kuma bada ceto.

A ranar 29 ga wata da karfe 6 da safe, aka fuskanci aukuwar gocewar kasa a wani wurin hakar ma'adini mallakar kamfanin Huatailong na kasar Sin dake garin Mozhukunggar na yankin Tibet. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu, ma'aikata 83 ke binne a karkashin kasa. Gwamnatin yankin Tibet mai cin gashin kanta da kamfanin da abin ya shafa suna yin kokarin ceton su. Ya zuwa karfe 10 da safe na ranar 30 ga wata, ba a gano mutane ko kuma samun gawawwaki a wurin ba, ana ci gaba da kokarin ceton jama'a. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China