in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kyautata tsarin zirga-zirgar jiragen sama na jihar Tibet
2015-04-07 15:52:07 cri
Bisa labarin da wakilinmu ya samu a ranar 7 ga wata daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na jihar Tibet mai cin gashin kanta, an ce, kwanan baya, babban filin jiragen sama na Gongga dake birnin Lhasa ya kaddamar da hanyoyin jiragen sama biyu, wato daga birnin Lhasa zuwa birnin Shanghai bisa hanyar birnin Chengdu, da kuma daga birnin Lhasa zuwa birnin Hangzhou bisa hanyar birnin Mianyan, ke nan, yawan jiragen sama da ke zirga-zirga a jihar Tibet a lokacin zafi da kaka na wannan shekara zai kai 310, abin da ya karu da kashi 11 cikin 100 bisa na bara.

Sakamakon ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma na jihar Tibet, bukatun zirga-zirgar jiragen sama sun karu sosai. Bisa labarin da aka bayar, an ce, kwanan baya, an kaddamar da hanyar zirga-zirgar jiragen sama daga birnin Guangzhou zuwa birnin Linzhi, da kuma daga birnin Lhasa zuwa birnin Kathmandu na kasar Nepal, hakan ya sa tsarin zirga-zirgar jiragen sama na jihar ya samu kyautatuwa, matakin kuwa zai ci gaba da inganta harkokin tattalin arziki, al'adu, da zamantakewar al'umma da ke tsakanin wannan jiha, da ma sauran wurare na kasar, har ma da sauran kasashen dake makwabtaka da ita.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China