Yu wanda ya bayyana hakan a yankin Tibet na kasar Sin, ya kuma yi kira da a rika warware matsaloli bisa doka tare da gudanar da harkokin Ibada bisa tsarin addinin Buddah.
Ya kuma bayyana matsayin kasar Sin na ci gaba da sanya kafar wando guda da masu kokarin kawo mata baraka ta kowace fuska.
Jami'in ya ce, za a dauki wannan mataki ne bisa doka ta yadda za a samar da zaman lafiya a yankin da kuma hadin kai a kasa baki daya. (Ibrahim)