in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ba ta hana 'yancin bin addini a Tibet ba
2015-03-04 20:23:59 cri
Kwanan baya, wani marubucin kasar Faransa Maxime Vivas wanda ya yi suna a kasar Sin sakamakon littafin da ya rubuta mai suna "ainihin halin Dalai Lama" ya bayyana cewa, yana shirin fito da littafinsa na biyu game da al'adu da kuma addini a yankin Tibet na kasar Sin, domin kara fahimtar da mutanen duniya game da yadda al'amura ke gudana a zahiri a yankin

Mr. Vivas ya ce, ya dade yana shirya littafin. Kafin ya je Tibet a shekarar 2010, ya sami dukkanin bayanai dangane da yankin daga kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya, inda suka nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta lalata al'adun Tibet, ta kuma hana 'yancin bin addini a yankin. Amma bayan ya zo yankin, ya ga ko ina an lika talla, alamun hanyoyi a harshen Tibet, sa'an nan ya ziyarci wasu makarantu, inda ya ga ana karatu da kuma rubuta a harshen Tibet, haka kuma, ko ina akwai gidajen ibada da kuma masu yin addu'a.

Bayan ya ziyarci yankin Tibet, Mr.Vivas ya gano cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta hana 'yancin bin addini a Tibet ba, a zahiri yana ganin cewa, gwamnatin kasar tana da hakuri a fannin bin addini, sabo da a wasu yammacin kasashe, kamar a kasar Faransa, ana hana wasu abubuwan da suka shafi addini a fili. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China