Bayanin ya bayyana yadda shekaru 50 da suka wuce kawo yanzu, kafuwar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bude wani sabon babi, ta yadda jama'ar yankin suka zama mutane masu dogaro da kai, suka mike daga halin matalauci zuwa yanayin wadata, da kuma sauyi daga yanayin rufe kofa zuwa bude kofa.
A cikin shekaru 50 da suka gabata, bisa jagorancin kwamitin tsakiyar JKS, da kuma goyon baya daga daukacin jama'ar sauran yankunan kasar Sin, da kokarin jama'ar jihar Tibet, an cimma burin hada kan al'ummomi, da samun jituwar zaman al'umma, tare da samun babban ci gaba wanda ba a taba ganin irinsa ba kafin aiwatar da kwaskwarimar demokuradiyya.
Bayanin ya nuna cewa hakan muhimmin sauyi ne a tsarin gurguzu mai matukar fifiko. Kaza lika tsarin kulawa da jihohi, da al'ummomi da kansu, tsari ne da ya dace, wanda kuma aka yi amfani da shi wajen daidaita batun al'ummomi a kasar Sin. (Fatima)