in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada matsayin Tibet na yanki mai cin gashin kansa
2015-09-06 10:52:49 cri

Mahukuntan kasar Sin sun fidda wata takardar sanarwa, wadda ke jaddada matsayin yankin Tibet, na kasancewarsa yanki mai cin gashin kansa, gabanin bikin cika shekaru 50 da fara aiwatar da wannan manufa.

Takardar wadda aka yiwa lakabi da "Cimma nasarar manufar cin gashin kan yankin Tibet,", ta bayyana cewa, tun bayan aiwatar da manufar sauyi ta shekarar 1959, da kuma baiwa yankin na Tibet damar cin gashin kai a shekarar 1965, yankin ya samu zarafin aiwatar da zamantakewa mai ma'ana, ya kuma cimma manyan nasarori a fannin bunkasa tattalin arziki.

Kaza lika yankin ya samu nasarori masu yawa wadanda ke da fa'ida ga al'ummun dake zaune cikin sa, ciki hadda dunkulewar da yankin ke yi da sauran sassan kasar Sin, matakin da kuma ke kara haifar da ci gaba mai dorewa, da kuma daidaito tsakanin al'ummun kasar Sin baki daya.

A daya hannun kuma, takardar ta tabo batun makarkashiyar da Dalai Lama da 'yan kanzagin sa ke yi, game da yayata bukatar neman cikakken 'yancin yankin na Tibet, matakin da a cewar takardar ya sabawa doka, yana kuma haifar da koma baya ga ci gaban yankin.

Takardar ta ce, matakin da Dalai Lama ya dauka, ya ci karo da muradun al'ummar Tibet, wanda hakan ne ma ya sanya bai samu goyon bayan al'ummar yankin ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China