A yau ne ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta kara bai wa wuraren jihar Tibet da girgizar kasa ta shafa bargunan zamani dubu 20 da kuma kwat-kwata din auduga dubu 20.
Wannan taimako na zuwa ne sakamakon shawarar da tawagar da ke jagorantar ayyukan rage radin bala'i a karkashin shugabancin majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar da kuma kokarin biyan bukatun jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar na yaki da bala'i,
Baki daya ma'aikatar ta bai wa wadannan wurare tantuna dubu 20, kwat-kwata din auduga dubu 50, bargunan zamani dubu 50, gadajen tafi da gidanka dubu 15, jakunkunan shiga domin barci dubu 15.
Girgizar kasa da ta abku a kasar Nepal ta rutsa da wasu sassa na jihar Tibet ta kasar Sin, a yanzu haka sojojin kasar Sin fiye da dubu 5 suna himmatuwa wajen rage radadin wannan bala'in a Tibet. (Tasallah Yuan)