Hukuma mai kula da jiragen saman jigilar fasinjoji ta yankin na Tibet ta bayyana cewa, ya zuwa Talatar nan hukumar ta bude sabbin hanyoyin sufuri 9, ciki hadda wadda take tsakanin Lhasa zuwa Lijiang, ta hakan yawan hanyoyin zirga-zirgar jiragen suka kai 48.
Kaza lika an fara bude zirga-zirga tsakanin sabbin birane 6, da suka hada da birnin Zhengzhou, da Lijiang da sauransu, wanda hakan ya kara yawan biranen da ake zirga-zirga tsakaninsu da Tibet zuwa 33.
A wadannan shekarun da suka gabata, an gaggauta bunkasa sha'anin zirga-zirgar jiragen sama na yankin Tibet, matakin da yake da nasaba da bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa, da hada-hadar tattalin arziki da cinikayya.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan mutanen da suka ziyarci yankin Tibet a shekarar 2014 ya kai miliyan 15, adadin da ya karu da kashi fiye da 20 cikin dari bisa na shekarar 2013. (Zainab)