Takardar ta bayyana cewa, yankin Tibet kashi daya ne na kasar Sin, kuma kabilar Tibet tana daya daga cikin kabilun kasar Sin. Yankin Tibet ya dauki wannan hanyar raya yankin ta yanzu, wanda wadda ta dace da bunkasuwar al'adu da zamani, da zamantakewar al'ummar dan Adam, da halin da ake ciki a kasar Sin, da kuma moriyar jama'ar yankin Tibet daga 'yan kabilu daban daban.
Hakazalika kuma, takardar ta yi nuni da cewa, yankin Tibet ba zai samu kyakkyawar makoma ba sai dai idan an tsaya tsayin daka kan hadin kai, da kokarin neman samun ci gaba da zaman lafiya, da kuma yaki da ayyukan ra'ayin barakaaware da koma baya da kuma rikice-rikice. (Zainab)