An zuba jari da yawansa ya kai Yuan biliyan 6 don gina gidajen jama'a ga mutanen dake fama da talauci a yankin Tibet
Bisa labarin da hukumar gina gidaje da raya birane da kauyuka ta yankin Tibet ta bayar, an ce, an zuba jari da yawansa ya kai Yuan biliyan 6 a shekarar 2014 don gina gidajen jama'a ga mutanen dake fama da talauci a yankin. An fara gina gidajen kusan dubu 72 a shekarar 2014, kuma an kammala gina yawancinsu a halin yanzu, lamarin da ya bada damar kara kyautata yanayin zaman rayuwar mutane kimanin dubu 100 a wannan yankin.
Shugaban gwamnatin yankin Tibet ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnatinsa a gun taro na 3 na wakilan jama'ar yankin karo na 10 da aka gudanar a kwanakin baya, inda ya yi nuni da cewa, yawan mutanen da aka kyautata yanayin zaman rayuwarsu a shekarar 2014 ya kai dubu 94 da dari 7.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a shekarar 2014, gwamnatin yankin Tibet ta samar da kudi Yuan miliyan 47.5 ga iyalai masu fama da talauci wajen yin haya gidaje, domin taimaka musu warware matsalarsu ta muhallin zama. (Zainab)