in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa dake jihar Tibet a kalla 20 sun mutu sakamakon girgizar kasar Nepal
2015-04-27 14:46:57 cri

Ya zuwa daren jiya, babbar girgizar kasar da ta fadawa Nepal a ranar asabar 25 ga wata, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 20 a birnin Shigatse dake jihar Tibet na yammacin kasar Sin, tare da bacewar wasu 4, da jikkatar wasu 58, gami da sake tsugunar da mutane kimanin 24,803.

Bisa labarin da aka samu, an ce, sakamakon babbar girgizar kasar ta Nepal, gidaje 1206 ne suka rushe a birnin Shigatse ta jihar Tibet, sannan wassu gidajen ibada 54 sun rugurguje. Ya zuwa yanzu, an tura masu aikin ceto 17000 birnin Shigatse.

A ranar 26 ga wata, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na Sin ya kebe kudaden da yawansu ya kai Yuan miliyan 30 ga hukumar jihar Tibet cikin gaggawa, don sake gine-gine a yankunan da bala'in ya rutsa da su da farfado da muhimman ababen more rayuwa a wurin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China