Mahalarta taron kula da cinikayya da samar da bunkasuwa na MDD, sun amince da wani rahoto, wanda ya bayyana irin bambancin manufofi dake akwai, tsakanin kasashe daban-daban a nahiyar Afirka, matakin da a cewar rahoton, ke haifar da cikas ga bunkasuwar sana'ar ba da hidima. Rahoton ya kuma bayyana cewa, shawarwarin dake gudana game da yarjejeniyar cinikayya maras shinge a Afrika, za su taimaka wajen samar da dama ta daidaita manufofin kasashen daban-daban, da bunkasa sana'o'i daban-daban.
Bisa wannan rahoto, an ce, sana'ar ba da hidima ta samu bunkasuwa da kashi 4.6 cikin dari, daga shekarar 2009 zuwa 2012, cikin wannan adadi akwai fannin sufuri, da na adana kayayyaki, da fannin sadarwa da dai sauransu, wadanda suka samu bunkasuwa mafi sauri.
Ban da haka kuma, rahoton ya ce, daidaita manufofin ba da hidima a Afrika zai taimaka wajen bunkasa fannin, tare da samar da guraben aikin yi.
Kaza lika rahoto ya jaddada wajibcin daidaita manufofi tsakanin kasashe daban-daban dake nahiyar ta Afrika ta fuskar hada-hadar kudi, da samar da manyan ababen more rayuwa. Har wa yau ya nuna yadda hidimomin da ake bayarwa ta fuskar manyan ababen more rayuwa, ciki hadda samar da ruwa, da na'urorin kiwon lafiya da sauransu, ke da babbar mana'a ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa wanda MDD ta tsara. (Amina)