Shugabannin kasashen Afrika sun amince da kaddamar da shawarwari kan kafa wani yankin kasuwanci bisa 'yanci na nahiyar nan zuwa nan da shekarar 2017, bayan sun rattaba hannu a makon da ya gabata kan wata yajejeniyar da ke da nufin kafa wani babban yankin kasuwanci bisa 'yancin da ke kunshe da kasashe 26.
Shugaban kungiyar tarayyar Afrika (AU) a wannan karo, kana shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya ba da sanarwa a ranar Litinin a yayin taron kungiyar AU a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu cewa, an bude shawarwari kan yankin kasuwanci bisa 'yanci na nahiyar (CFTA). (Maman Ada)